Home / KUNGIYOYI / Duniya Ta Yi Koyi Da Ayyukan Gidauniyar A A Charity

Duniya Ta Yi Koyi Da Ayyukan Gidauniyar A A Charity

 

Daga Imrana Abdullahi

A kokarin da gidauniyar taimakawa al’umma ta A A Charity keyi domin ganin al’amura sun ci gaba da habbaka ta yadda jama’a za su amfana yasa jagora baki daya wadda ta samar da gidauniyar tare da wata tawagarta suka kai ziyara gidan Gwamnatin jihar Kano a arewacin tarayyar Najeriya.
 Alhaji Shehu Wada Sagagi, shugaban ma’aikatan gidan Gwannatin jihar Kano tare da Honarabul Jamilu Abubakar Danbatta, mai bayar da shawarar na musamman a kan harkokin yada labarai duk sun yi murna da jin irin muhimman abubuwan da Gidauniyar A A Charity ke aiwatarwa domin inganta rayuwar al’umma.
Kuma sun yi alkawarin yin aikin hadin Gwiwa da wannan Gidauniya mai kokarin taimakawa dukkan al’umma baki daya.
Dukkannin jami’an Gwamnatin biyu da kuma jakadiyar zaman lafiya Hajiya Dokta Aminatou Abdoulkarim Muhammad sun tattauna irin yadda za a samu yin aikin hadin Gwiwa tsakaninsu bisa ayyukan Gidauniyar A A Charity da Gwamnatin Jihar Kano.

Tun da farko Jakadiyar zaman lafiya Hajiya Dokta Aminatou Abdoulkarim Muhammad ta yi wa jami’an Gwannatin cikakken bayanin irin ayyukan da Gidauniyar ke yi da suka hada ta kulawa da biyan ilimin marayu, koyawa mata sana’o’i, taimakawa gajiyayyu da sauran ayyukan jinkai da jama’a ke bukatarsu duk da nufin samun ingantacciyar al’umma.

Ta kuma yaba da irin matakan da Gwannatin jihar Kano ke dauka domin Farfado da batun tattalin arzikin jama’a.

Dukkan bangarorin biyu sun amince da samun wadansu wurare ko bangarorin inganta rayuwar jama’a da za su yi aikin hadin Gwiwa a game da su da suka hada da batun rage radadin talauci,Samar da ayyukan yi, Tallafawa jama’a su dogara da kansu, taimakawa mabukata da gajiyayyu da kuma masu bukata ta musamman da ke cikin al’umma.

About andiya

Check Also

RE: ALLEGATION OF EXTORTION BY OFFICER OF THE NGERIA CUSTOMS SERVICE FEDERAL OPERATIONS UNIT ZONE ‘B’ AT MOKWA AXIS OF NIGER STATE

      (1) The Comptroller Federal Operations Unit Zone ‘B’ Kaduna, Comptroller Dalha Wada …

Leave a Reply

Your email address will not be published.