Home / Labarai / EFCC Ta Gayyaci Tallen, Tsohuwar Minista

EFCC Ta Gayyaci Tallen, Tsohuwar Minista

Tsohuwar ministar ma’aikatar da kula da harkokin mata Uwargida Pauline Talken ta je hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ranar Juma’a don amsa tambayoyi kan zargin karkatar da kudi naira biliyan Biyu (2)  a lokacin da take kan mulki.

An ruwaito Tallen, ta isa ofishin hukumar EFCC shiyyar Abuja amma har yanzu babu cikakken bayani kan zargin da ake yi wa tsohon ministar, wata majiya mai tushe ta ce tana iyaka da cin hanci da rashawa har naira biliyan biyu.

An yi zargin an karkatar da wani bangare na kudaden ne daga wata kungiya mai zaman kanta ta Afrika (AFLPM).

Maryam Abacha, tsohuwar uwargidan shugaban Najeriya ce ta jagoranci wannan shiri wanda ya shafi samar da zaman lafiya da lumana a Afirka.

Idan dai za a iya tunawa jim kadan kafin ranar 29 ga watan Mayu, hukumar EFCC ta ce ta na da niyyar bin gwamnonin da ke barin gado da sauran jami’an gwamnati.

 A wani labarin kuma a ranar Alhamis ne hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta gayyaci tsohon gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi bisa zargin karkatar da naira biliyan hudu.

Binciken dai an ce yana da nasaba ne da yadda ake tafiyar da kudade a lokacin da yake gwamnan jihar Ekiti.

Fayemi ya ce an gurfanar da shi ne a kan “koken da bai dace ba daga wata kungiya mara fuska, wadda ake kira Ekiti Patriotic Coalition”, ya kara da cewa “a shirye ya ke ya ba da cikakken hadin kai.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.