Home / Labarai / KWANKWASIYYA TA FARA RUSHE RUSHE A KANO

KWANKWASIYYA TA FARA RUSHE RUSHE A KANO

Daga Imrana Abdullahi
Duk da irin halin matsin tattalin arzikin da al’ummar Najeriya Najeriya shiga ciki sai ga Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin zababben Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya samu nasarar lashe zabe karkashin jagorancin jam’iyyar Kwankwasiyya ta NNPP da tsohon Gwamnan Jihar Kano Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso.
Ita dai wannan jam’iyya ta NNPP kamar yadda kowa ya Sani dimbin Talakawa ne suka taru ya hanyar bayar da cikakken hadin kai da goyon baya har Gwamna Abba Kabir Yusuf ya samu damar darewa kan ragamar Gwamnatin Jihar Kano da ya kayar da Gwamnatin APC mai mulki a Jihar Kano da kasa baki daya, tun a zamanin mulkin Buhari.
Sai kawai a  jiya Juma’a cikin Dare, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP, ya jagoranci rusa wasu gine-gine a filin sukuwa.
Rahotannin suka ci gaba da bayanin cewa rusau din ya rutsa da wasu shaguna 90 ne da aka gina ba bisa ƙa’ida ba a filin sukuwa na Race Course da ke Nasarawa.
Dama dai tun a jawabinsa na rantsuwar kama aiki a ranar May 29, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya soke duk wani gini da aka yi a filayen gwamnati ba bisa ka’ida ba.
Kazalika ya kuma bai wa jami’an tsaro ikon kula da su, tare da sa idon Hukumar tsara Birane ta Jihar Kano (KNUPDA).
Kamar yadda wasu majiyiyi suka bayyana, Gwamnan ya fara kaddamar da rusau din ne a wani ginin da ke kan titin filin sukuwa a Kano.
Tun kafin a zabe shi, Gwamnan ya yi alkawarin yin rusau a kan wasu gine-gine da aka yi ba bisa ka’ida ba.
Tun bayan da Gwamnan na NNPP da shi ne daya till da ya samu nasarar lashe zabe  Jihar kwaya daya, amma sai ga shi an fara Saka da irin yadda ya fara a yanzu.
Rabi’u Musa Kwankwaso dai ya yi takarar shugaban kasa ne a karkashin jam’iyyar NNPP kuma ana saran ko a nan gaba za a zai sake neman tsayawa takara kuma ya na bukatar Talakawa da daukacin masu hannu da shuni su bashi cikakken hadin kai da goyon baya a batun samun nasara.

About andiya

Check Also

APC National Chairman, Ganduje Commissions Road Named After Him in Gombe

  …Lauds Governor Inuwa’s Examplary Leadership …Says “President Tinubu, APC Leadership Proud of Gombe Governor’s …

Leave a Reply

Your email address will not be published.