Home / Labarai / AKWAI BUKATAR MANIYYATAN JIHAR BAUCHI SU BAYAR DA CIKAKKEN HADIN KAI

AKWAI BUKATAR MANIYYATAN JIHAR BAUCHI SU BAYAR DA CIKAKKEN HADIN KAI

DAGA IMRANA ABDULLAHI
Buƙatar hakan ta fito ne daga bakin shugaban kwamitin yaɗa labarai na kwamitin Amirul Hajji Alhaji Yayanuwa Zainabari, ya yin da ya gudanar da taron Manema labarai kan halin da ake ciki da nasarori da aka samu game da tashin Maniyatan jiha zuwa ƙasa mai tsarki.
Shugaban kwamitin ya ce gwamnatin Jihar Bauchi ƙarƙashin Sanata Bala Abdulƙadir Muhammad ta samar da duk  abin da ake ɓuƙata domin samun nasarar aikin hajji Alhazan jihar.
 sai ya ɓuƙaci Maniyatan da su ci gaba da bada haɗin kai ga kwamitin domin samun nasarar aikin tun daga nan gida har zuwa can ƙasa Mai tsarki.
Alh. Yayanuwa yace kwamitin Amirul Hajji da Jami’an hukumar Alhazai ta jiha da na tarayya suna kan aiki ba dare ba rana wajen ganin dukkan ministan jihar Bauchi su isa kasar Saudiyya zuwa ranar 7 ga watan Yuni ko ma kafin ranar.
Yace dukkan Maniyatan da suka biya kudin su ta hannun hukumar Alhazan su kwantar da hankalinsu ba wani wanda za’a bari da yardan Allah kuma nan bada jimawa Jirgi na biyu ma zai tashi.
Sai yayi godiya wa Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulƙadir Muhammad kan goyon Bayan da yake basu domin samun nasarar mahajjatan jiha.
Jamilu Barau Daga Bauchi

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.