Daga Imrana Abdullahi kaduna
Gwamnan Jihar kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufa’i tare da Tawagarsa ya ziyarci yankunan kananan hukumomin Igabi da Giwa inda ya shaidawa duniya cewa ba za a daidaita da yan bindiga ba da ke daukar rayukan mutane.
A ranar Litinin ne dai Gwamnan tare da Tawagarsa suka ziyarci daruruwan da yan bindigar suka kai wa hari inda aka yi nasarar rayuka da duniya mai yawa.
Biyo bayan harin ne da aka kai a ranar Lahadia kauyen Kerawa yasa tawagar Gwamnatin ta je domin jajanta masu
Lamarin dai ya shafi mutane Kerawa, Zariyawa, Hashimawa, Wazata da sauran wadansu wurare a kananan hukumomin Igabi da Giwa.
Gwamnan ya tabbatar wa da mutane cewa babu batun daidaitawa da wadannan mutane yan bindiga, kuma za a ci gaba da aikin kakkabe dukkan batagarin da ke hai wa jama’a hari kasancewa jami’an tsaro a shirye suke.
Gwamnan ya bayyana matukar bakin cikinsa na salwantar rayukan da aka samu, ya kuma jinjinawa jami’an tsaron da suka bi samun yan bindigar tare da warhaka su baki daya.
Duk wannan na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun kwamishinan kula da tsaro da harkokin cikin gida Samuel Aruwan
A kauyen kerawa Gwamnan cewa ya yi
“Hakika wannan hali be mai warhaka kwarai na bakin ciki tare da tausayawa. A wannan kauyen kawai an binned Gawa 41 kamar yadda Limamin ya bayyana. A wani kauyen kuma annkai wa mutane 2 ko uku hari. Yan bindiga sun kaiwa wadannan kauyukan hari kuma sun salwantar da rayuka sanan an yi asarar dukiya mai yawa. Jami’an tsaro sun samu nasarar kai wa wadannan yan bindigar hari daga sama da kasa kuma mafi yawan yan bindigar tuni an shafe su”.
“Ina godiya ga sojojin sama da na kasa, Jami’an farin kasa sibil defens, yansanda da kuma jami’an yan sanda na farin kaya da suka hanzarta kai wa jama’a dauki. Akwai bakin ciki ganin yadda aka rasa rayuka, da abin ya fi haka muni idan da jami’an tsaro ba su kai dauki ba. Mun zo nan ne domin jajanta maku tare da yin ta’aziyya don haka muka kara yin kira ga jama’a da su kara hakuri tare da hada kai da jami’an tsaro”.
“Alhakin Kate dukiya da rayukan jama’a ya rataya ne a wuyana da abokan aiki baki daya”
Gwamnan ya kara jaddada wa mutanen cewa Gwamnati ba za ta daidaita da wadannan mutanen ba wato yan bindiga masu kashe mutane haka kawai.
” A kaduna mu ba zamu amince da ayyukan yan ta adda ba. Ba zamu nemi a sasanta da su ba, mun bayar da umarni ga jami’an tsaro da su sharesu baki daya. Wadannan yan ta addan ya dace ya bayyana su a matsayin yan ta adda kawai don haka ayi masu irin yadda ake yakin da Boko haram. Babu wata kafa ta batun a daidaita da duk wani dan bindiga mai kashe mutane”.
“Muna fatar wannan batu na yan bindiga zai kawo karshe domin kuwa jami’an tsaro na rungimar yaki zuwa ga yan bindigar. Muna iyakar bakin kokarinmu kuma zamu ci gaba da yin hakan. Don haka yana da kyau mutanen mu su kara hakuri su kuma ci gaba da yi mana addu’a. Allah be kawai ya iya kuma baya kuskure na Sani jami’an tsaro na yin bakin kokari kwarai”.