Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya bayyana samun hadin kai tsakanin ‘yan majalisun dokoki na kasa da ke jihar a matsayin abin da ya haifar da mai ido ta hanyar kawo ayyukan gwamnatin tarayya zuwa jihar Jigawa.
Gwmnan ya yi wannan tsokaci ne lokacin da ya jagoranci bikin kaddamar da tallafi karatu na naira miliyan 25 da dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Birnin kudu da Buji, Injiniya Magaji Da’u Aliyu, ya samar ga daliban manyan makarantu da suka fito daga mazabarsa.
Ya yi kira ga dan majalisar tarayyar ya ci gaba da fifita bukatun al’umma a zuciyarsa, sannan ya bada tabbacin kammala aikin babban asibitin Birnin kudu a wannan shekarar.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da babban mai taimakawa Gwaman Jihar Jigawa Auwal D Sankara ya sanya wa hannu.
A sakonsa ga taron, shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila wanda Gagarabadan majalisar, Alhaji Alhassan Ado Doguwa, ya wakilta ya bayyana Engineer Magaji Da’u Aliyu a matsayin jajirtaccen dan siyasa da ya cike gibin da ake samu na koma bayan ‘yan arewa wajen shiga a dama da su a hada-hadar majalisar kasa.
Daga nan sai ya yabawa Governor Badaru Abubakar saboda manufarsa ta bunkasa aikin gona da samarwa matasa ayyukan yi, inda yayi nuni da cewa kamata yayi duk dan siyasa ya kasance mai fafutukar kawo sauyi mai ma’ana ga alumma a maaimakon burin Tara kudi da alfarmar rayuwa.
A nasa jawabin, EngineerMagaji Da’u Aliyu, yace akwai kudurori biyu da ya gabatar dan neman kafa kwalejin ilimi ta tarayya ta musamman da Jami’ar ilimin wutar lantarki a kananan hukumimin Birnin kudu da Buji da aka yi wa karatu na daya da na biyu a zauren majalisar, inda ya bukaci Gwamna Badaru Abubakar ya taimaka wajen ganin kudurorin sun zamo dokar da za ta sahale gudanar da ayyukan guda biyu.
Sauran wadanda suka yi jawabai sun hadar da shugaban jam’iyar APC na jihar Jigawa Alhaji Habibu Sani Sara, da shugabannin kananan hukumomin Birnin kudu da Buji.
Bikin ya samu halartar mataimakin gwamnan Umar Namadi da sakataren gwamnatin jiha da wakilan majalissar dokoki na kasa da sukia fito daga jihohin Kano, Bauchi, Niger da kuma Cross Rivers