Home / Big News / El-Rufai Ya Karya Dokar Sallamar Ma’aikata Da Masu Zaman Haka Kawai – RATTAWU

El-Rufai Ya Karya Dokar Sallamar Ma’aikata Da Masu Zaman Haka Kawai – RATTAWU

El-Rufai Ya Karya Dokar Sallamar Ma’aikata Da Masu Zaman Haka Kawai – RATTAWU
Mustapha Imrana Abdullahi
Shugaban kungiyar masu aiki a kafafen yada labarai, dirama da wasan kwaikwayo na tarayyar Nijeriya Kwamared Dokta Kabir Garba Tsanni ya bayyana Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru Ahmad El- Rufa’i a matsayin mutumin da ya yi dokar Sallamar ma’aikata karan tsaye sakamakon son zuciyarsa kawai.
Kwamared Dokta Kabir Garba Tsanni ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai Kaduna.
“Hakika El- rufa’i ya taka dokar aikin kwadago game da sallamar ma’aikata da masu zaman haka kawai, saboda haka babu wanda zai amince da hakan”, inji shugaban RATTAWU na kasa.
Ya ci gaba da bayanin cewa su na fatan Gwamnan zai yi amfani da abin da doka ta tanada domin yin abin da ya dace fa kowa in kuma ba haka ba za mu ta fi yajin aikin kasa baki daya kawai, Iowa ya huta.

About andiya

Check Also

Shekara Ɗaya A Ofis: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Muhimman Ayyuka A Wasu Ƙananan Hukumomin Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Ƙananan Hukumomin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.