Home / Labarai / El- Rufa’i: Za A Kwace Mani Fili A Kaduna

El- Rufa’i: Za A Kwace Mani Fili A Kaduna

Daga Abdullahi Abdullahi Kaduna

An Yi Kira Ga Gwamna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i da ya Sanya baki sakamakon wani mutum da ke kokarin kwace wa wata mata fili a Unguwar Danhonu a karamar hukumar Chkun cikin Jihar Kaduna.

Matar mai suna Malama Fiddausi ta yi koken ne cewa akwai wani mutum mai suna Suleiman A U Abdullahi, da ake kira da “Cif detel” da ke kusa da Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’I, shi ke neman ya kwace wa Malama Firdausi Filinta a Unguwar Danhonu cikin Kaduna.

Ita dai Malama Firdausi, ta bayyana koken ta ne ga manema labarai a Kaduna, inda ta zargi na kusa da Gwamnan Jihar Kaduna mai suna Suleiman A U Abdullahi, da cewa ya handame mata filinta da ke Unguwar Danhonu a cikin karamar hukumar Chikun Jihar Kaduna.

Malama Firdausi ta ce “Ina da dukkan takardun Gwamnati da a tsarin dokar Filaye da gini yakamata mutum ya mallaka duk Fiddausi ta tabbatarwa da manema labarai cewa ta na da su”.

“Ina da takarda tun daga ta wurin Mai Unguwa,Dagaci,Hakimi da dukkan hukumomin Gwamnati da dokar Jihar Kaduna ta ce sai mutum ya tanada duk na mallakesu amma kuma sai ga wani mai suna Suleiman A U Abdullahi ya lashe Mani fili na da a yanzu ya Dora gininsa a kan wanda na fara tun asali”, inji Fiddausi.

Ta kara da cewa sakamakon hakan ne nake yin kira ga Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i da ya taimaka ya karbo Mani hakki na daga wannan mutum da ke aiki a kusa da shi.

“Saboda sun ce mana wai Gwamna ne da kansa ya Karbe wurin ya bashi Suleiman A U Abdullahi, da yake aiki tare da shi amma kuma na san a kokari da kuma adalcin mai girma Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i ba zai yi hakan ba, ya karbi fili na a matsayin mara karfi talaka ya mikawa wani duk da ina da takardun da ya dace in mallaka a bisa dokar Jihar Kaduna, wato takardun mallakar fili da ta hukumar yin gini ta Jihar Kaduna”.

Fiddausi dai ta kawo kukanta ne ga manema labarai da nufin ko Allah zai sa a dace bukata ta biya nufi Gwamna Malam Nasiru na Kaduna ya taimake ta a kwato mata hakkin ta daga wajen wanda take zargi Suleiman A U Abdullahi.

Kamar dai yadda ta shaidawa manema labarai a Kaduna cewa ” wani makwancinta ne ke neman kwace Mani fili na, kamar yadda ta ce wai ya ce Gwamna ne ke ya hade masa da filinsa duk da cewa ta na da dukkan takardun mallakar filin na dukkan hukumomi a Jihar Kaduna. A hukumance hukumar Filaye da ta mai bayar da izinin gini ta KASUPDA duk sun san ina da filin, hatta ma takardun regularazation ma da duka raba ma ni an ba ni nawa.

Lauya na ya rubuta masu korafi a kan hakan amma har wa’adin da ya ba su ya kare ba tare da sun ce masu komai ba, na kuma kaiwa shugaban kwamitin wanda shi ma ya rubuta ya ce an kaiwa Gwamna da mataimakiyar Gwamna da ofishin hukumar Filaye ta Jihar Kaduna, Amma ban Sani ba ko koken ya kai ga Gwamna ko bai kai ba ni ban Sani ba”.

Da take amsa tambayar shin ko hukuma ce ta rushe wa Fiddaisi Fili sai ta ce ba hukuma ba ce ta rushe gininta, ma’aikata kawai shi wanda ake zargi ya dauka ya je ya rushe mata fili haka kawai domin kawai a yadda muke gani ya na amfani da rigar Gwamna ne kawai aga cewa shi ma’aikaci ne a bangaren Gwamnati kuma ya ce shi ne Cif detal na Gwamna da suna kamar haka Suleiman A U Abdullahi, kuma ya na yin hakan ne domin kawai ya cutar da ni kawai domin na tabbata ba Gwamna ba ne ya Karbe fili na ya hada masa ba”.

Sai dai a bisa bayanan da muka samu daga wajen matar ta ce ta na kokarin tafiya kotu ne a halin yanzu domin neman hakki na wanda hadi da hakan ne na kawo koke na a wajen yan jarida domin su sanarwa da duniya.

“Ina son ne Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i ya ji wannan koken nawa domin ya taimake ni saboda dukkan hanyoyin da dokar Jihar Kaduna ta tanada da mutum ya dace ya bi game da batun Filaye duk na bi hanyoyin baki daya.

Hakika ina fatan Gwamna ya taimake ni domin ni ba ni da karfi saboda shi wannan mutum na shiga cikin rigar Gwamna ya na cewa an Karbe an bashi filin don haka ina son a taimake ni saboda in har ya Karbe wannan wurin ban san yadda zan yi da rayuwa ta ba shi ya sa a matsayina  na talakar Jihar Kaduna nake kai koke na gare shi a matsayin Gwamna mai cikakken iko da ke da wuka da Nama a hannunsa, a taimake ni a dubi kuka na a cikin wannan lamarin”, inji Fiddausi.

Da wakilinmu ya tuntubi wanda ake zargi Suleiman A U Abdullahi, sai ya ce wannan lamari fa na bin doka da oda ne kamar yadda kowa ya Sani don haka ya dace yan jarida masu bincike su ta fi wurin hukumomin da alhakin aikin ya shafa domin samun sahihai kuma ingantaccen bayani sosai.

Da aka tuntubi mai magana da yawun hukumar Filaye ta Jihar Kaduna, sai ya ce zai kira wanda ya tuntube shi din domin jin ta bakinsa.

Kuma duk abin da ya biyo baya zaku ji shi a nan gaba.

Da wakilin mu ya je hukumar bayar da izinin yin ginin gidaje ta Jihar Kaduna KASUPDA mai magana da yawun hukumar Nuhu Garba Dan Ayamaka, cewa ya yi su hukumarsu ba ta batun maganar fili sai izinin yin gini saboda haka wannan mata idan ta ce ta na da dukkan takardun sai ta ta fi kotu kawai.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.