Home / Labarai / Rashin Bashir Tofa a wannan lokaci babba hasara ce ga yan Nijeriya, inji Iyorchia Ayu

Rashin Bashir Tofa a wannan lokaci babba hasara ce ga yan Nijeriya, inji Iyorchia Ayu

Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, Dr Iyorchia Ayu ya baiyana bacin ransa da jimami dangane da rasuwar Alhaji Bashir Tofa tare da baiyana cewar, ba shakka yan Nijeriya sun yi rashi adali dan siyasa mai hangen nesa da son talakawa.
‘Bashir Tofa dattijo ne a kalamansa da huldarsa, nayi hasara abokin shawara, mutum mai hikima da raha tare da maraba a tsakaninmu don sadar da sakon da zai amfani al’umma cikin adalci da gaskiya ga kowane bangare na kasarnan” Inii Iyorchia Ayu
Ya nemi al’ummar jahar Kano da na Arewa da kasa baki daya dasu sanya iyalai da yan uwan Marigayi Tofa cikin addu’oinsu sakamakon wannan rashin mai girma na dattijo, zarumi, dan kishin kasa, mutum mai taimakon al’umma da tsare gaskiya a zantukansa da hulda da kowa, mussaman daga cikin yan siyasa Nijeriya.
Dr Ayu ya baiyana Marigayi Tofa da kasancewa namijin duniya da bai da fargaba ga baiyana abin da ya dace da aikata hakan gaban kowa don ciyar da al’ummarsa da kasarsa a gaba tare da neman hadin kai.
Baya ga gabatar da ta’azziyarsa ga iyalai da sauran yan uwa da masoya al’umma Nijeriya ya kira tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, Alhaji Umar Ghali Na’abba don sadar da sakon ta’azziya da rokon Allah Ya gafarta masa da mafificin alherinsa da rahama a kabarinsa.

About andiya

Check Also

WE MUST DEPLOY ADVANCED TECHNOLOGY TO FIGHT INSECURITY, GOVERNOR LAWAL TELLS UNITED NATIONS 

By; Imrana Abdullahi, Kaduna Governor Dauda Lawal has emphasized the pressing need to deploy advanced …

Leave a Reply

Your email address will not be published.