Daga Imrana Abdullahi
Daukacin talakawan Najeriya na kara kokawa da irin yadda ake samun matsalar tashin farashin kayan amfanin Gona yun daga ainihin garuruwan da ake Noma amfanin da suka hada Funtuwa, Dandume, Faskari’ Sabuwa, Malumfashi, Kafur da Bakori wadannan duk a cikin Jihar Katsina suke, duk suna Noman Shinkafa, Dawa, Alkama, Auduga, Yalon Bello, Gauta, Kubewa da kuma Rogo da duk wadannan abubuwan da Talakawa ke Nomawa amma a yanzu na neman su gagari talakawan kasancewa su ne daman dan abincin da talakawan ke samu suna Sanya wa a bakin salati cikin sauki amma a yanzu saboda matsalar tsadar farashin kayan abinci Talakawa fa sun shiga cikin wani mawuyacin hali.
Daga cikin wadannan kayan amfanin Gona akwai wani abu ko in ce wadansu abubuwan da a can baya farasinsu ba wani abu ba ne da ke gagarar talakawa kar irin su Dankali, Kubewa, Yalon Bello da Gauta kai har ma da Rogo da ba kowa yake damuwa da cinsa ba a nan kasar hausa duk da cewa ana yin Nomansa a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas, amma sai ga shi a yau farashinsa ya kai..
Banda garuruwan da ke Noman Gero da Dawa da kuma farin Wake da suka hada da yankin Daura da Katsina.
Da wakilin mu ya tuntubi wadansu masu sana’ar sayar da Hatsi kuma da suka kasance manoma a garin Funtuwa da kuma masu shagunan sayar da Hatsin a cikin Unguwanni, sun tabbatar mana da cewa a kasuwar jiya Litinin a garin Funtuwa an sayar da Masara dubu 55,000, Dawa dubu 52,000 sai buhun Waken Soya naira dubu 37,000 a kan kowane buhu daya.
Amma a yau Talata kasuwannin Faskari da Bakori duk da suke a Jihar Katsina an sayar da Buhun Masara duk daya naira dubu 60,000 sai Dawa dubu 55,000 Waken Soya kuma naira dubu 37,000, shi kuma farin Wake an sayar da shi naira dubu Hamsin da Bakwai zuwa da Takwas.
Kuma Tiyar Masara a cikin Unguwanni ana sayar da ita naira dari shida wasu kuma shida da Hamsin wanda ku san wasu shagunan sayar da Hatsi ake sayar wa ku san kudi daya.
Da muka tuntubi wani mai shagon da yake sayo Hatsin a wadannan kasuwanni ya kawo shagon sa ya sayar wa da jama’a kuma nan da nan ya kada baki ya ce hakika ni Masara da Dawa har ma da Farin Wake a halin yanzu duk sun fi karfi na domin ban iya sayo su har in ce zan sayar.
Ya ci gaba da cewa Buhun busasshen farin Rogo da tun shekaru da yawa muke sayo shi naira dubu 17,000 a yanzu ya kai naira dubu 37,000 kuma ba a ma samunsa ko an je kasuwar wato dai ya yi karanci.
Hakalika da wakilin mu ya tuntubi wani mai Nikan inji da yake da Injunan Casar hatsi da Shinkafa da kuma Nikan kayan amfanin Gona su koma gari cewa ya yi, ” Wallahi yunwa ta kama jama’a saboda a wannan lokacin duk cikin kwaryar Nikan da za a kawo guda Goma sai mu ga guda Takwas ko Tara duk sai an Sanya masu farin Busasshen Rogo wanda a can baya ba abin da jama’a za su yi da Rogo amma a halin yanzu ya zama abinci”.
Haka shima wani mai sana’ar Cajin wayoyin hannu na mutane cewa ya yi a duk lokacin da mutane suka kawo mana Cajin irin koke – koken da suke yi kasan akwai yunwa wallahi a tare da jama’a, domin akasarin su suk za su rika koken cewa ba su ta ba shiga yanayin babu da talauci mai tsanani irin na yanzu ba.
Sai kuma wuraren da ake Noman Masara Dawa, Dankali da Jar Masara, Shinkafa da dai sauransu duk wuraren nan amfanin Gonar tsada yake yi sosai.
Sabida haka ake ganin in dai za a rika samun tsada a inda ake Noman hatsi to ina ga irin su Legas, Fatakwal da yankin Kudu maso Yamma da ake kai wa Hatsi daga arewacin Najeriya inda ake Nomansa.
Akwai wani mutum da ya shaida Mani cewa ko a cikin garin Kaduna ana sayar da Tiyar Masara a kan kudi naira dari Takwas da Hamsin kudin Tiyar Wake kuwa tuni ta tasamma dubu biyu a duk tiya daya.
Farashin buhunan hatsi yau ranar Talata abin ba dadin ji ga talaka, yayin da buhun masara ƙwara ɗaya ya haura naira dubu sittin N60,000 yau a kasuwar Faskari.
Ku dubi irin wanna farashin nawa ne kudin masu dakon lodawa da sauke wa da kuma kudin motar da masu safarar Hatsin za su biya? Sannan su kuma nawa za su sayar har su samu riba? Sai kuma Talakan da bashi da komai yake fama da babu a halin yanzu yaya zai yi ya samu abinci a kalla sau uku rana da irin wannan tsadar Hatsin da manoman arewacin Najeriya ke Nomawa?
Kuma wani babban al’amari shi ne wai tambaya a nan yaya mutanen kasashen Nijar, Kamaru, Chadi da sauran kasashen Turai da wasu kasashe a Nahiyar Asiya da kasar Cana da ke samun Masara da Waken Soya daga Najeriya kuma suke sarrafa shi ta hanyoyi daban daban.
Me kuke tunanin ya jawo ɗan karen tsadar da ba a taba samunta ta hatsi kamar wannan lokacin ba?
Za mu kawo cikakken rahoton farashin hatsin a kasuwanni daban daban.