Home / News / Majalisar Katsina Ta Nemi Agajin Gaggawa Ga Wadanda Ruwan sama Ya  Yi Wa Barna 

Majalisar Katsina Ta Nemi Agajin Gaggawa Ga Wadanda Ruwan sama Ya  Yi Wa Barna 

….Sama da gidaje 50 ne ruwan sama ya lalata 

Daga Imrana Abdullahi

Majalisar dokokin Jihar Katsina ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tallafa wa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a karamar hukumar Dutsi da ke jihar.

Bayanan da aka samu zuwa ga majalisar Sama da gidaje 50 ne ruwan sama ya lalata a yankin.

Majalisar ta yi wannan roko ne yayin zaman majalisar na ranar Talata.

An yi wannan kiran ne biyo bayan wani kudiri na gaggawar wayar da kan jama’a da Abduljalal Isma’il mai wakiltar mazabar Dutsi ya gabatar a gaban majalisar.

Mista Isma’il ya ce, “A Daren Asabar, ruwan sama da ya dauki tsawon sa’o’i ana yi ya lalata gidaje, gonaki, dabbobi, da wasu wuraren kasuwanci.”

Ya ci gaba da cewa yayin da sama da gidaje 30 suka lalace a Unguwar Dan-Haune, sama da gidaje 20 sun lalace a Unguwar Dutsi.

Don haka, ya yi kira ga majalisar da ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta bayar da tallafin gaggawa ga wadanda abin ya shafa “domin samun saukin halin da suke ciki”.
Bayan tattaunawa kan lamarin, majalisar ta umarci magatakarda da ya rubutawa bangaren zartarwa na gwamnati don shiga tsakani.

Majalisar ta kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin titi mai tsawon kilomita 40 daga Maraban Kankara zuwa karamar hukumar Danja.

An yi wannan kiran ne biyo bayan kudirin da dan majalisa mai wakiltar mazabar Kafur Shu’aibu Wakili ya gabatar.

A cewar Shu’aibu Wakili, hanyar da aka bayar a shekarar 2020, ya kamata a kammala ta cikin watanni shida amma daga baya aka yi watsi da ita.

Ya bayyana hanyar a matsayin mai mahimmanci kuma “babba domin hanya ce mai sauki wacce masu ababen hawa ke bi ta Kaduna da Abuja da sauransu”.

Da yake yanke hukunci kan gudunmawar da mambobin majalisar, Kakakin majalisar, Nasir Yahaya-Daura, ya yi, alkawarin cewa majalisar za ta yi duk mai yiwuwa don ganin an kammala aikin cikin gaggawa.

A karshen tattaunawar da ’yan majalisar suka yi, majalisar ta kuma umurci magatakardar da ya mika wa gwamnatin jihar shawarar ta a rubuce.

About andiya

Check Also

Q1: More Nigerians buy Dangote Cement, as volume rises by 26.1% to 4.6MT 

  Strategies adopted by Dangote Cement to increase sales and ensure an adequate supply of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.