Home / Ilimi / Fito Na Fito Da Gwamnati Bashi A Tsarin Musulunci – Shaikh Sambo Rigachikun

Fito Na Fito Da Gwamnati Bashi A Tsarin Musulunci – Shaikh Sambo Rigachikun

Fito Na Fito Da Gwamnati Bashi A Tsarin Musulunci – Shaikh Sambo Rigachikun

Mustapha Imrana Abdullahi
Sanannen Malamin addinin Musulunci mataimakin shugaban kungiyar Izala ta kasa bangaren Jos Shaikh Yusuf Sambo Rigachikun ya bayyana cewa ba dai dai bane yin fito na fito, Zanga Zanga ko yi wa Gwamnati tawaye.
Shaikh Yusuf Sambo Rigachikun ya bayuana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna.
Yusuf Sambo ya ce hakika dukkan wadannan abubuwan da aka lissafa na yi wa Gwamnati tirjiya ba su a tsarin addinin Islama, amma dai ya dace mutane da kuma ita kanta Gwamnatin ta lura da wadansu abubuwa.
“Idan da Kamar yadda aka zabi wannan Gwamnatin karkashin Buhari yadda shi kansa ya yi farin jini a wajen mutane wanda saboda hakan jama’a da dama suka bayar da cikakkiyar gudunmawarsu domin ganin an samu nasara, hakika wannan abin la’akari ne”.
Rigachikun ya kuma yi bayanin cewa yanayi da halin davale ciki wata yar manuniya ce da ya dace Gwamnatin da kanta ta yi la’akari da yadda abin yake domin samun ingantacciyar nasarar da kowa ke bukata.
Malam Rigachikun ya ankarar da Gwamnati bukatar dauke akwai na ta hanzarta daukar matakan yin shawara da tattaunawa da jama’a musamman yin shawara da wadanda suka taimaka ko bayar da gudunmawarsu har aka samu nasarar da ake takama da ita a halin yanzu.
“Ga kuma tsofaffin shugabannin kasa masu rai kamar irinsu Ibrahim Badamasi Babangida, Abdussalamu Abubakar, Shonekan,Jonathan, Olusegun Obasanjo da sauransu domin a tsara shawara a samu nasara a tafiyar da kasa”.
Ga kuma wadansu mutane da suka rike manyan mukamai a kasa irinsu Aliyu Muhammad Gusau, ha tsofaffin mataimakan shugabannin kasa, da za a kira su a kalla duk wata a tattauna shawarwari da su kowa zai bayar da tasa shawarar domin ci gaban kasa.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.