Home / Labarai / An Kama Mutane 11 Game Da Wasoson Kaduna – Samuel Aruwan

An Kama Mutane 11 Game Da Wasoson Kaduna – Samuel Aruwan

An Kama Mutane 11 Game Da Wasoson Kaduna – Samuel Aruwan
Imrana Abdullahi
Kwamishinan kula da tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Kaduna Malam Samuel Aruwan, ya bayyana cewa Gwamnati ta kama mutane Goma sha daya (11) da aka samesu da laifukan kwasar kaya.
Samuel Aruwan ya ce cikin wadanda aka kama akwai wani da aka samu da Gadon kwanciya, wasu kuma sun zo da motar daukar kaya, wasu kuma sun shiga shagon Dinki sun kwashe kayan dinkin da aka ba mai dinki, wasu kuma sun je wurin ajiyar kaya na wani kamfani a kusa da kamfanin hada motoci na Fijo, inda yan son zuciya suka kwashe Waken soyan sa aka Sanya wa magani.
Samuel Aruwan ya ci gaba da cewa abin da Gwamnati ta bankado shi ne ana labewa da Guzuma ne domin a harbi Karsana kuma Gwamnatin ba za ta bari ba.
Ya kuma yi kira ga iyaye da su kara mayar da hankali wajen tarbiyyar yayansu, saboda kamar yadda ya ce ana samun matsalolin rashin tarbiyyar yara da a can baya babu irin hakan.
Ya ce babu wani jami’in Gwamnati da ya ajiye wani kaya a wani wuri domin kashin kansa domin yin wani abin son zuciya, kaya ne da kwamiti ya ajiye a wani gida kuma za su raba shi a matsayin rabon kayan kashi na uku kamar yadda aka raba a baya, kuma gidan da aka ajiye babu mutane a ciki.
Samuel Aruwan ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da kafar yada labarai ta Talbijin da rediyo DITV a cikin shirin Me Ya Faru?
“Wannan kayan abincin da aka ajiye a wani Gida na Karamar hukumar Chikun ne kuma su suka nemi a ba su gidan domin kwamitin ya raba kayan nan a sati mai zuwa”.
Samuel ya kuma kara jan hankalin jama’a da su kara ba Gwamnati cikakken hadin kai da goyon baya kasancewar mai rikon kujerar Gwamnan Jihar Kaduna ta yi wa jama’a jawabi.
“Saboda da ba a dauki matakin da aka dauka ba kamar yadda jami’an tsaro suka ba Gwamnati shawara da sai wani ko wasu idan sun taso daga Zariya zuwa wani wuri ko Kafanchan zuwa wani wuri za a iya tare mutum ayi masa ba dai dai ba don haka daukar matakin shi ne abin da ya dace”.

About andiya

Check Also

NASCON grows turnover by 37%, assures Shareholders of Continuous Growth, Value Creation

NASCON Allied Industries Plc has assured its shareholders of continuous growth and value creation in …

Leave a Reply

Your email address will not be published.