Home / News / Ganduje Ya Kori Kwamishina Saboda Murnar Mutuwar Abba Kyari

Ganduje Ya Kori Kwamishina Saboda Murnar Mutuwar Abba Kyari

 

Kwamishinan da ke Lura da ma’aikatar ayyuka da gidaje na  jihar Kano, Engr. Muazu Magaji ya nuna farincikinsa da rasuwar shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari.

A rubutu da ya dinga yi na nuna farincikinsa, a ranar Asabar, Muazu Magaji ya bayyana cewar “Abin farin ciki guda biyu, Najeriya ta kubuta, Abba Kyari ya mutu da Annoba”.

Kwamishinan ya kuma bayyana cewar shi bai iya munafurci ba, dan haka dole ya fito fili ya nuna farincikinsa kan rasuwar Abba Kyari, a cewarsa.

Mutane da dama a cikin da wajen jihar Kano suka kalubalanci wadannan kalamai na kwamishinan da ya yi a kan Abba Kyari, inda wasu ke kira ga Gwamnan Kano, Alhaji Abdullahi Umar Ganduje da ya koreshi daga mukaminsa saboda cin amana ne abin da ya yi.

Har ya zuwa lokacin hada Wannan rahoto, Engr. Muazu Magaji na ci gaba da yin kalamai na nuna murna da farinciki kan rasuwar, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.