Home / KUNGIYOYI / Gidauniyar A A Charity Ta Karrama Boss  Mustapha

Gidauniyar A A Charity Ta Karrama Boss  Mustapha

 

Daga Imrana Abdullahi

Sakamakon kula da irin dimbin ayyukan taimakon al’umma da kungiyar taimakawa marayu, gajiyayyu da koyawa dimbin jama’a sana’o’i da Gidauniyar A A Charity ta lura tsohon Sakataren Gwamnatin tarayya a lokacin Gwamnatin Muhammadu Buhari Boss Mustapha keyi yasa kungiyar ta Karrama shi da lambar Yabo mai girma.

Gidauniyar A A Charity ta lura sosai da irin ayyukan taimakon da Boss Gado Mustapha ke aiwatarwa da nufin ciyar da al’umma gaba, a wajen babban taron kaddamar da sababbin Jagororin Gidauniyar da kuma bayar da tallafi ga marayu da bayar da tallafin yin sana’a sai Gidauniyar ta Karrama tsohon sakataren.

A wajen taron Boss Mustapha, ya samu wakilcin Iniiniya Nimrod Maniyunda Musa ya wakilta ya kuma karbi lambar yabon a madadin tsohon sakataren Gwamnatin tarayyar a karkashin jagorancin Muhammadu Buhari

Jim kadan da yake tattaunawa da manema labarai bayan karbar shaidar karramawar Injiniya Nimrod Maniyunda Musa cewa yana da kyau a rika taimakawa marayu da gajiyayyu domin abu ne mai kyau kwarai da gaske.

Injiniya Nimrod ya kara da cewa suk wanda ya taimakawa mabukaci lallai Allah zai taimaka wa mutum, saboda haka ne nake yin kira ga daukacin al’umma musamman masu hannu da shuni da su taimakawa jama’a, sakancewar duk arzikin mutum akwai rana mai zuwa da mutum zai bar arzikin ya ta fi gudan gaskiya ko mutum yaki ko yaso hakan sai ta faru.

A game da taimakawa jama’a ta fuskar wasanni kuwa sai Injiniya Nimrod Maniyunda Musa ya ce ” koda yake Naga a halin yanzu an ba shugaban kwallon Kwando Musa Kida lambar Yabo, ai hakan ta faru ne sakamakon taimakon da yake yi wa jama’a musamman ta fuskar wasanni shi yasa wannan Gidauniya ta bashi lambar Yabo domin cika aikinsa.

“Abin da zan gaya maku shi ne yanzu a nan Kaduna musamman ma yan wasan kwallon Gora a cikin kulab din marayu ne da yawa kuma a yanzu sun je kasashen Afirka da yawa. Kuma wani abin sha’awa shi ne ba abin da zai iya tara mutane wuri daya kamar wasanni. Misali a wajen wasan da aka yi tsakanin Najeriya da Kamaru ba a nuna wani bambancin harshe ko daya ba, ka ji inda aka ce Bayarabe ko bahaushe?

Injiniya Nimrod ya kuma ce ba shakka harkar wasanni za ta iya taimakawa wajen rage matsalar tsaro.

Kuma, ” a yanzu idan ni da kaina na cewa yaran unguwar Rugasa su fito duk zaka gansu a a wajen sun fito, idan an bani kasa da awa 24 zan tara yaran Rigasa domin suna jin maganar mu sosai kuma ba kudi zan ba su ba, da an ce masu ga wane ne ke son a fito harkar wasanni za su fito. Amma kai dan siyasa zaka kawo kudi amma ni ba zan kawo ko Kwabo ba”.

Ya ce alamace ta aikin da suke yi domin ciyar da harkar wasanni gaba ta Sanya a yanzu Gwamna Uba Sani zai bayar da kudi naira biliyan biyu domin gyara filin wasanni na Ahmadu Bello Kaduna, don haka muke yin kira ga daukacin jama’a da suka amfana da wannan tallafin da su koma suma su taimaka wa wasu a cikin al’umma.

About andiya

Check Also

Q1: More Nigerians buy Dangote Cement, as volume rises by 26.1% to 4.6MT 

  Strategies adopted by Dangote Cement to increase sales and ensure an adequate supply of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.