Home / Labarai / Gidauniyar Zaman Lafiya ta horar da mata hanyoyin kasuwanci tare da tallafa musu da jari
Shaikh A Maraya making a Presentation to one of the beneficiaries

Gidauniyar Zaman Lafiya ta horar da mata hanyoyin kasuwanci tare da tallafa musu da jari

Gidauniyar Zaman Lafiya ta Duniya (GPF) ta horar da mata 40 hanyoyin kasuwanci inda ta baiwa kowace jarin naira dubu 10 don fara aiwatar da kananan sana’o’ a masarautar Kaninkon da ke karamar hukumar Jama’a ta jihar Kaduna.

Yayinda yake jawabi a wajen bayar da horon da aka gudanar a Unguwan Fari da ke masarautar Kaninkon, shugaban Gidauniyar ta kasa, Rabaran John Joseph Hayab, yace manufar shirin shine bunkasa hanyoyin zaman lafiya tsakanin musulmi da kirista dake zaune a masarautar ta hanyar bunkasa hanyoyin kasuwanci.

“Manufarmu shine bunkasa zaman lafiya ta hanyoyin tattalin arziki da kasuwanci kuma muna fatan hakarmh ta cimma ruwa, domin bincike ya tabbatar hanya mafi sauki na alkinta zaman lafiya shine ta hanyar kasuwanci da ya shafi saye da sayarwa.”inji shi

Hayab, ya kara da cewa an kafa gidauniyar zaman lafiyar ne don kawar da duk wani bambamce-bambamce dake tsakanin mabiya addinai domin a cewarsa, ” dukkanmu iyali guda karkashin Ubangiji.”

Ya kara da cewa fiye da shekaru biyu da suka gabata suna zuwa wannan yanki na Kaninkon kan maganar samar da zaman lafiya biyo bayan tashin hankalin da aka samu a yankin a wancan lokacin.

“Bayan tsawon shekaru biyun da muka shafe muna zuwa kan maganar zaman lafiya da alama mun comma nasarar haka domin ga shi mun ga alamar haka a tare daku musulmai da kirista kuna samun fahimtar juna a nan.

“Daya daga cikin darussan da muka koya dake dada nisanta mutane da juna shine rashin abinda zai hada su waje daya, kuma mun gane wannan abin ba komai bane face harkokin kasuwanci.” Ya bayyana

Yace sun fara basu jarin karamin kudi ne saboda su fara gwada su da kananan sana’o’i irinsu tuyan kosai da alale da doya da gyada da sauransu don ganin gudun ruwansu a kai da kuma yadda zasu amfanar da sauran zuwa wani lokaci.

Yayinda yake nashi jawabin, shugaban gidauniya da ke kula da yankin arewacin Najeriya, Sheikh Halliru Abdullahi Maraya ya hori matan da su yi amfani da dan abinda suka samu don juya shi a kasuwanci ba ta wata hanyar daban ba, don samun babban jari nan gaba.

Yace tallafin ya game dukkanin kabilun yankin ba tare da banbancin addini ba.

Yayinda yake tofa albarkacin bakinsa, Sarkin Kaninkon, Mallam Tanko Tete, kira yayi ga matan da su ririta jarin da aka basu don samun ninkin ba ninkin nan gaba, domin a cewarsa, da rarrafe yaro kan tashi.

A karshe yayi kira ga Gidauniyar da su ci gaba da kokarin da su ke yi wajen ayyukan bunkasa zaman lafiya da xi gaba a yankinsa.

Wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin sun nuna gidiyarsu da Gidauniyar da ta zabo su cikin daruruwan mabukata don farawa da su ta hanyar basu horo da kuma tallafa musu da jari a kai.

Sannan sun yi kira ga sauran kungiyoyi da daidaikun masu hali da su yi koyi da gidauniyar wajen tallafawa mabukata.

About andiya

Check Also

Tinubu Appoints Silas Ali Agara DG NDE

By Ibraheem Hamza Muhammad President Bola Ahmed Tinubu has approved the appointment of Honourable Silas …

Leave a Reply

Your email address will not be published.