Home / Ilimi / GOBARA TA KONE MAKARANTAR LIMAN SA’IDU FUNTUWA

GOBARA TA KONE MAKARANTAR LIMAN SA’IDU FUNTUWA

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
BAUANAN da muke samu daga cikin garin Funtuwa Jihar Katsina sun tabbatar mana cewa wata mummunar Gobara ta Kone kusan dukkan shahararriyar  makarantar Liman Sa’idu da ke Unguwar Dutsen reme.
Ita dai wannan makarantar ta Liman Sa’idu Funtuwa ita ce ta farko da aka fara ginawa da ta kasance babbar makarantar gaba da sakandare da ake karantun ilimin samun shaidar takardar NCE.
Kuma ita ce wadda ake karatun Sakandare, gaba da Sakandare da suka hada da karatun Boko da na addinin musulunci, wanda dalibai suke kwana a makarantar kuma bayanan da muke samu ana samun dalibai har daga Janhuriyar Nijar da dukkan sassan Najeriya.
Amma bayanan da muke samu a yanzu Gobarar da ta tashi wanda ya zuwa rubuta wannan labarin an samu asara kwarai da Gobarar ta lashe a kalla kusan kashi Casa’in na wannan shahararriyar makarantar da ta yaye dimbin dalibai bisa tafarkin Sunnar Manzon Allah S A W.
Da fatan Allah ya kiyaye faruwa hakan a nan gaba ya kuma mayar da Alkairi amin summa amin.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.