Home / Lafiya / Gwamnan Zamfara Ya Amince Da Gyarawa Da Inganta Asibitin Kwararru Na Yariman Bakura Da Ke Gusau

Gwamnan Zamfara Ya Amince Da Gyarawa Da Inganta Asibitin Kwararru Na Yariman Bakura Da Ke Gusau

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya amince da shirin gyara, tare da sake inganta asibitin ƙwararru na Yeriman Bakura da ke Gusau domin magance ƙalubalen da ake fuskanta na samar da ingantacciyar kiwon lafiya a Jihar Zamfara.
Gwamnan ya amince da aikin gyaran asibitin ƙwararrun ne a ranar Litinin a taron Majalisar Zartarwa karo na sha tara a gidan gwamnati da ke Gusau.
A wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya bayyana cewa za a fara aikin gyaran ne nan take, kuma ana sa ran gyaran zai mayar da asibitin zuwa babbar cibiyar lafiya ta zamani kuma mai isassun kayan aiki irin na zamani.
A cewar sanarwar, an yanke wannan shawarar ne a daidai lokacin da aka ayyana dokar ta-ɓaci a ɓangaren kiwon lafiya na Zamfara.
Ya ce, “A jiya lokacin da Gwamna Lawal ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa, ya amince da yadda za a yi gaggawar gyara asibitin ƙwararru na Yeriman Bakura.
“Asibitin ƙwararru na jihar ya daɗe a lalace kuma ba shi da isassun kayan aikin kiwon lafiya. Hakan ke tilasta majiyyata yin tattaki zuwa Sakkwato ko Kaduna domin samun wankin ƙoda da sauran gwaje-gwajen lafiya.
“Alhaji Mustapha Falaki, Shugaban Cibiyar Minjirya Health Services Limited, ya gabatar wa majalisar koke kan halin da asibitin ƙwararrun ke ciki a halin yanzu da kuma matakan da za a ɗauka na sake fasalin cibiyar.
“A cikin shirin gyaran asibitin, za a gina sabbin gine-gine da wuraren kiwon lafiya, za a samar da na’urorin kiwon lafiya, sannan a  horar da masu amfani da na’urorin don mayar da asibitin ƙwararru ya zama wurin kiwon lafiya na zamani da ingantattun kayan aikin da za su samar da ingantacciyar kiwon lafiya ga al’ummar jihar.
A yayin taron majalisar, an tattauna batutuwa masu muhimmanci da dama. Ɗaya daga cikin manyan batutuwan da aka tattauna shi ne manufofin jin daɗin jama’a a zamantakewar jihar. Wannan manufar na da nufin haɗa kan al’umma daban-daban na Jin Ɗadin Jama’a waɗanda suka dace da hangen nesan Jihar Zamfara a matsayin ɗaya daga cibiyar ci gaban al’ummar Nijeriya. Manufar ita ce tsare-tsare don taimakawa wajen jagorantar zuba jari na jama’a da masu zaman kansu don Jin Daɗin Jama’a a zamantakewa.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.