Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya amince da biyan ma’aikatan Jihar kuɗaɗen su na hutu a matsayin wata garaɓasa ta musamman albarkacin watan Ramadan.
A ranar Laraba ne ma’aikatan gwamnatin Jihar da na Ƙananan Hukumomi a Zamfara suka fara karɓar kuɗaɗen hutu.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar a Gusau, ta bayyana cewa kuɗaɗen hutun ma’aikatan shi ne kashi 10 cikin 100 na albashin su na shekara.
A cewar sa, kuɗaɗen hutun da aka biya a matsayin kyautar azumin Ramadan wani shirin jin daɗi ne da aka bai wa dukkan ma’aikatan gwamnati domin sauƙaƙa wahalhalun tattalin arzikin da ƙasar ke fuskanta.
Sanarwar ta jaddada cewa gwamnatin Gwamna Lawal ta kasance mai son ma’aikata. “Bayan hawansa mulki, Gwamna Lawal ya biya duk albashin da ma’aikata ke bin gwamnatin da ta shuɗe, ya kuma biya kuɗaɗen garatuti, sannan ya amince da biyan albashin watanni 13 ga ma’aikatan jihar.
“Saboda yanayin matsin tattalin arzikin da ƙasar nan ke ciki, Gwamna Lawal ya nuna jin daɗin sa da ƙwazon ma’aikatan gwamnati da masu riƙe da muƙaman siyasa. A matsayin sa na mai alheri, ya amince da biyan kuɗin hutu ga duk ma’aikata.
“Gwamnan ya jajirce wajen kyautata jin daɗin ma’aikatan gwamnati, tare da tabbatar da samun albashi da alawus a kan lokaci. Biyan kuɗin hutun wani alami ne na kulawar da Gwamnan ke nuna wa al’ummar Jihar Zamfara.
“Gwamnati ta riga ta biya kuɗaɗen hutu ga ma’aikatan Jiha da Ƙananan Hukumomi da ’yan fansho. Bugu da ƙari, masu riƙe da muƙaman siyasa, su ma sun samu garaɓasar kuɗin da zai taimaka musu a cikin watan Ramadan.”