Home / Uncategorized / Gwamna Dauda Lawal Ya Jajantawa Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Gumi

Gwamna Dauda Lawal Ya Jajantawa Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Gumi

Daga Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jajanta wa waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Ƙaramar Hukumar Gummi ta jihar.
Ambaliyar ta afku ne a sanadiyyar ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka lafka a ranar Juma’ar da ta gabata a wasu yankunan Ƙaramar Hukumar Gummi, inda ta rutsa da gidaje da dama.
A wata sanarwa da mai magana da yawun sa, Sulaiman Bala Idris ya fitar ranar Asabar, gwamnan ya nuna matuƙar damuwa tare da jajanta wa waɗanda ambaliyar ta shafa ta Gummi.
Sanarwar ta ƙara da cewa,, “Na samu labari mai firgitarwa game da ambaliyar ruwa a wasu sassan ƙaramar hukumar Gummi. Wannan lamari ya yi matuƙar ɗaga min hankali, kuma ina tare da duk waɗanda abin ya shafa.
“Na tuntuɓi hukumomin da abin ya shafa, da shugabanni, da dattawa a ƙaramar hukumar tun bayan faruwar lamarin.
“Nan take na aika da tawaga daga gwamnatin jihar Zamfara zuwa ƙaramar hukumar domin duba halin da ake ciki tare da bayar da agajin gaggawa ga waɗanda abin ya shafa.
“Gwamnatina ta ƙuduri aniyar ɗaukar dukkan matakan da suka dace don hana afkuwar irin wannan lamari na baƙin ciki nan gaba. Dukkanin hannuwa za su kasance a wuri guda don tabbatar da cewa wafanda ambaliyar ruwan ta shafa sun sami tallafin da ya dace da za su buƙata.”

About andiya

Check Also

Bafarawa Ya Kaddamar Da Kungiyar Matasa Domin Ceton Arewa Da Najeriya Baki Daya

….Mu Bamu da wata matsala da kowa, inji Bafarawa Imrana Abdullahi A wajen wani babban …

Leave a Reply

Your email address will not be published.