Home / Uncategorized / Gwamna Dauda Lawal Ya Yaba wa Godwin Obaseki

Gwamna Dauda Lawal Ya Yaba wa Godwin Obaseki

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yaba wa Gwamna Godwin Obaseki kan yadda ya kawo sauyi da kuma ƙudirinsa na inganta fannin kiwon lafiya na Jihar Edo.
Gwamnan ya kasance babban baƙo a wajen bikin ƙaddamarwa, rantsar da sababbin ɗalibai da kuma cika shekaru 60 da kafa Kwalejin Kimiyyar Kiwon Lafiya da Fasaha ta Edo (EdoCOHEST) da aka gudanar a birnin Benin a ranar Larabar da ta gabata.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa bayan ƙaddamar da kwalejin, gwamnonin sun zagaya da kayayyakin zamani da aka samar a ginin.
A lokacin da yake gabatar da jawabinsa, Gwamna Lawal ya ba da shawarar cewa jihohin biyu su kafa shirin musayar ɗalibai, wanda zai bai wa ɗalibai mata da ke makarantun kiwon lafiya a Zamfara damar zuwa kwalejin Edo domin yin wani zagon karatu.
Ya ce, “Haƙiƙa babban abin alfahari ne da kuma gata kasancewata a nan wurin tare da ɗan uwana da mutanen kirki na jihar Edo don buɗe wani sabon babi na Kwalejin Kimiyyar Kiwon Lafiyar da Fasaha ta Edo, musamman ga ɗaliban da suka shigo yanzu.
“Yayin da muka taru a nan, ina jinjina irin hangen nesa da jajircewar ɗan uwana Gwamna Obaseki, wanda ya sake farfaɗo da fata a Jihar Edo cikin kyakkyawar manufa, za a iya samun ɗaukaka duk da rashin daidaito a ƙasarmu mai albarka.
“Lokacin da na samu bayanai game da wannan ingantaccen aikin gaba ɗaya, na yaba kuma na jinjina wa ɗan uwana kan irin wannan manufa da za a iya cimmawa kaɗai ta bangaren juriya, hangen nesa da sadaukarwa.
“Ga ɗaliban da suka shigo a yau, zan ce ku ne burinmu kuma alfaharinmu. Kuna wakiltar jihar Edo da ƙasar mu gaba ɗaya ne. Don haka kada ku iyakance kanka.
“Ku yi karatu kuma ku yi fice a karatun; ku daraja aikin da ɗan uwana ya yi a yau don kanku da ɗalibai a nan gaba.
“Baya ga samar da ƙwararrun masana kiwon lafiya, ina addu’a cewa wannan kwaleji ta zama wata gada ta haɗa kan jama’a, samar da ayyukan yi, da bunƙasar tattalin arziki a ciki da wajen jihar Edo. ”
Gwamna Obaseki ya gode wa Gwamna Lawal bisa girmama gayyatar da mutanen jihar Edo suka yi masa.
“Ina matuƙar godiya da kai ɗan uwana Gwamnan Jihar Zamfara, Dokta Dauda Lawal da ka zo min wannan biki mai bangarori uku, wanda ya hada da ƙaddamarwa, rantsar da sabbin ɗalibai, da kuma  cika shekaru 60 da kafa Kwalejin Kimiyyar Kiwon Lafiya da Fasaha ta Edo (EdoCOHEST).”

About andiya

Check Also

Dangote Hails Tinubu on Impact of Crude for Naira Swap Deal

      …As Dangote Refinery partners MRS to sell PMS at N935 per litre …

Leave a Reply

Your email address will not be published.