Home / Labarai / GWAMNA DAUDA LAWAL YA YI TIR DA HARIN DA AKA KAI BUNGUDU

GWAMNA DAUDA LAWAL YA YI TIR DA HARIN DA AKA KAI BUNGUDU

DAGA IMRANA ABDULLAHI

Gwamnan jihar Zamfara,Dokta  Dauda Lawal, a ranar Litinin, ya kai ziyara Bungudu inda ya  yi tir da kakkausar murya kan harin da ‘yan bindiga suka kai a karamar hukumar Bungudu.

A daren jiya ne ‘yan bindiga suka kai hari a karamar hukumar Bungudu, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum daya tare da yin garkuwa da wasu mutane shida.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya ce gwamnan ya je Bungudu ne domin jajantawa masarautar da al’ummar karamar hukumar.

Ya kara da cewa Gwamna Lawal ya ziyarci fadar Sarkin ne domin tabbatar da aniyar gwamnatinsa da kuma shirye-shiryen kawo karshen matsalar ‘yan fashi a Jihar.

Ya ce: “Gwamna Dauda Lawal ya kasance a fadar Mai Martaba Sarkin Bungudu, Alhaji Hassan Attahiru, OFR domin jajanta wa Masarautar da daukacin al’ummar karamar hukumar bisa wannan mummunan harin da ‘yan bindiga suka kai.

“Gwamna Lawal a lokacin da yake jawabi a fadar, ya tabbatar da cewa nan ba da dadewa ba ‘yan fashi za su zama tarihi a fadin Jihar baki daya.

“Ya bukaci jama’a da su dage da addu’o’i domin yaba wa kokarin gwamnati na ganin an magance matsalar rashin tsaro, ya kara da cewa tsaro aikin kowa ne kuma yana bukatar hadin kai sosai.

“Ya kuma jajantawa iyalan mamacin tare da addu’ar Allah ya mayar da mutanen da aka sace.”

Sarkin Bungudu, Alhaji Hassan Attahiru, ya godewa gwamnan bisa ziyarar ta’aziyyar da ya kai masa.

Ya bayyana cewa Gwamnan ya nuna jajircewa tun bayan faruwar lamarin.

“Sai da sassafe mai martaba ya kira ni domin ya jajanta mana, ya kuma sanar da ni cewa ya bayar da umarni ga jami’an tsaro na ganin an gaggauta ceto wadanda lamarin ya shafa.” Inji shi.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.