Home / Labarai / Gwamna Dauda ya bayyana alhinin mutuwar Shugaban Bankin Access, Herbert Wigwe

Gwamna Dauda ya bayyana alhinin mutuwar Shugaban Bankin Access, Herbert Wigwe

Daga Imrana Abdullahi
Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana mutuwar Shugaban Bankin Acces, Herbert Wigwe, a matsayin babban rashi ga harkar banki a Nijeriya.
Idan dai ba a manta ba, Herbert Wigwe ya mutu tare da matarsa da ɗansa a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a California kusa da kan iyakar Nevada da ke Ƙasar Amurka.
A wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a Gusau ranar Lahadi, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana alhininsa kan rasuwar Herbert Wigwe da iyalansa.
A cewarsa, mutuwar Wigwe babban rashi ne ba ga iyalansa da abokansa kaɗai ba, har ma da ’yan kasuwa a ƙasar da ma nahiyar Afirka baki ɗaya.
“A game da mutuwar Wigwe, na rasa aboki wanda ya ba da gudunmawa sosai ga harkar banki a Nijeriya.
“Herbert Wigwe ya bar giɓin da ba za a taɓa iya cike shi ba a harkar banki a Nijeriya ta hanyar jajircewarsa.
“Ya bayar da ɗumbin gudunmawa ta hanyar ƙwarewarsa da ya amfani ’yan kasuwa da dama.
“Ina da dangantaka mai ƙarfi da Wigwe tun zamanin da nake harkar banki.
“Allah ya ba dangi, abokai da abokan hulɗar Wigwe haƙurin jure wannan babban rashi da ba za a taɓa mantawa da shi ba,” in ji sanarwar.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.