Daga Imrana Abdullahi
Bayanan da muke samu daga Jihar Katsina na cewa Gwamna Malam Dikko Radda ya bada umarnin daukar malaman S-Power 7, 325 da suka ci jarabawa aiki na din din-din (permanent).
Kamar yadda muka samu zantawa da wadansu mutane na cewa tun farko daman irin abin da suke tsammanin Gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Dokta Dikko Umar Radda ta aiwatar domin ci gaban Jihar da al’ummarta baki daya.
“Kasancewar dukkan al’ummar da ake kokarin ganin ci gaban ta daman za a iya samun hakan ne ta hanyar sama masu da ilimi mai inganci da nagarta, ganin daman ilimi ne Gishirin zaman duniya”.
Hakan ta Sanya wadansu mutane ke fadin albarkacin bakinsu kamar haka, “tarihin Jihar Katsina ba a taba daukar malamai dubu bakwai a lokaci daya ba Sai wannan karon na Gwamnatin Dikko Umar Radda”.