Related Articles
Gwamna Ganduje Ya Jajantawa Mutanen Danbatta Game Da Mutuwar Mutane 16
Mustapha Imrana Abdullahi
“Hakika mun Kadu tare da dimaucewa game da jin wani mummunan labarin mutuwar wadansu mutane Goma 16 yan asalin Danbatta da suke dawowa Kano daga Abuja a kan hanyarsu ta dawowa daga babbar hanyar Abuja – Kaduna, sun rasa rayukan nasu ne sakamakon harin da aka kai masu da wasu maharan da ba a san ko su waye ba”.
“Hakika wannan labari ya dimautar da mu domin muninsa da rashin dadin jinsa”
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da mai magana da yawun Gwamnan Jihar Kano Abba Anwar ya sanyawa hannu aka rabawa manema labarai.
Gwamnan Jihar Kano ne Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana hakan lokacin da yake jajantawa iyalan mutanen da suka rasa ransu da mutanen karamar hukumar Danbatta da mutanen Jihar baki daya game da rashin mutane 16 a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano kamar yadda lamarin ya faru.
” Allah ya gafarta masu ya kuma tona asirin wadanda suka aikata wannan aikin. Hakika babu wani abu mai tayar da hankali kamar wannan”, inji shi.
Sai ya shawarci jama’a da su ci gaba da yin addu’a domin samun saukin irin wannan lamari, ya kuma ba iyalan wadanda aka rasa rayukansu hakurin jure rashin”.
“A madadin Gwamnati da al’ummar Jihar Kano, ina jajantawa iyalan wadanda suka rasa ransu da jama’ar karamar hukumar Danbatta baki daya game da wannan gagarumin rashin da aka yi, Allah ya gafarta masu ya kuma saka masu bisa abin da suka aikata kyakkyawa n alkairi”,