Home / News / Hatsari Mutanen Kano 16 Suka Yi Ba Harin Yan Bindiga Ba – Samuel Aruwan

Hatsari Mutanen Kano 16 Suka Yi Ba Harin Yan Bindiga Ba – Samuel Aruwan

Hatsari Mutanen Kano 16 Suka Yi Ba Harin Yan Bindiga Ba – Samuel Aruwan
Mustapha Imrana Abdullahi
Mutane 16 yan asalin Jihar Kano hadarin mota ne ya kashesu ba harin yan bindiga ba a kan hanyar Kaduna Abuja.
Labarin da aka yi ta bayarwa a jiya cewa mutane yan asalin Jihar Kano su 16 ba yan bindiga ba ne suka kashe su ba, sun rasa rayukansu ne sakamakon hadarin mota da ya rutsa su a kan hanyar Kaduna- Abuja, hakika wanna labari ba haka yake ba kamar yadda aka rika yadawa tun a Jiya.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun kwamishinan kula da harkokin tsaro da al’amuran cikin gida na Jihar Kaduna Malam Samuel Aruwan.
Batun gaskiya a nan shi ne mutane 16 da suka mutu har lahira sun rasu ne sakamakon hadarin motar da ya rutsa da su a Rigachikun a kan hanyar Kaduna zuwa Zariya sun kuma samu hadarin ne sakamakon matsalar fashewar taya da suka samu a motar da suke ciki.
 Sakamakon hakan Gwamnatin Jihar Kaduna na mika sakon ta’aziyyarta ga iyalai da yan uwan wadanda suka mutu da fatan Allah ya jikansu ya gafarta masu kuma wadanda suka samu raunuka Allah ya kawo masu sauki cikin gaggawa
Hakika zamu yi bayani sosai idan bukatar hakan ta taso.
Ga layukan wayar karta kwana nan koda wani abu zai faru a inda kuke sai a tuntubi Gwamnati domin dauki: 09034000060
                                 08170189999

About andiya

Check Also

Our Mandate Is To Organise Congresses, Says Labour Party Transition Committee Chairman, Umar

  Former president of the Nigerian Labour Congress, NLC, and Transition Committee chairman of the …

Leave a Reply

Your email address will not be published.