Home / MUKALA / Gwamna Masari: Nijeriya na bukatarka a MAJALISAR DATTIJAI

Gwamna Masari: Nijeriya na bukatarka a MAJALISAR DATTIJAI

….Gwamna Masari: Nijeriya Na bukatarka A
MAJALISAR DATTIJAI

 

 

Jawabi ga manema labarai akan bukatar Mai Girma Gwamna Aminu Bello Masari ya fito takarar kujerar Sanata a zaven 2023 wanda Kakakin Qungiyar, Mohammad Lawal Maikuxi ya gabatar a xakin taro na Al Hayatt da ke bimin Katsina a ranar Lahadi 15 ga Mayun 2023

Muna yi maku kyakkyawar maraba da godiya bisa amsa gayyatar da muka yi maku domin gabatar maku bukatunmu da sauran ximbin jama’ar Jihar Katsina da Nijeriya.

 

 

A halin da ake ciki, an buxe kakar hada-hadar siyasa domin zavukan 2023 a Nijeriya kuma masu sha’awar tsayawa takara a bisa muqamai daban-daban sun fito, wasu kuma na shirin fitowa domin a zave su. Masu tallar ‘yan takara kuma suna tallata hajojinsu ga ‘yan Nijeriya. Wannan abin farin ciki ne domin alamu ne da ke nuna cewa dimokiraxiyya ta fara zaunawa a Nijeriya.

 

 

Mu, Gamayyar Qungiyoyim Kishin Qasa reshen Jihar Katsina, muna cike da murna ganin yadda harkokin dimokiradiyya ke gudana, domin dama ce ga ‘yan Nijeriya su zavi mutanen da za su jagorance su bisa hasashen za su taimaka wajen kawo sauqin rayuwa.

 

Sai dai kuma muna da babbar damuwa a halin yanzu. Damuwarmu ita ce furucin da Mai Girma Gwamna Aminu Bello Masari ya yi a lokacin hirarsa da wata jarida a bara. Wato abin da Mai Girma Gwamna ya ce shi ne ba zai shiga takara a zaven 2023 ba.

 

 

Mun daxe muna nazari da tattauna wannan magana saboda abubuwa biyu. Abu na farko shi ne inda maganar ta fito, wato Mai Girma Gwamna, Alhaji Aminu Bello Masari. Ba mu bukatar bayanin cewa Alhaji Aminu Masari dattaijo ne ko a wane irin sikeli za ka xora shi. Dukkanmu mun sani cewa ya wuce shekaru 70 da haihuwa. Na biyu a yau ya share sama da shekaru 30 ana damawa da shi a farfajiyar siyasar Nijeiya bayan ajiye aikin gwamnati. Alhaji Aminu tsohon kwamshinan ayyuka ne a Jihar Katsina, zavavven wakili a majalisar tsarin mulki a 1994.

 

 

A 1999, Alhaji Aminu Masari na cikin waxanda suka kafa jam’iyyar PDP. Da aka buxe hada-hadar zave a 1999 ya yi yunqurin takarar zuwa Majalisar Dattijai amma wasu dalilai suka ratsa, ya haqura, ya tafi Majaiisar Wakilai ta Tarayya a matsayin wakilin qananan hukumomin Malumfashi da Qafur.

 

 

A zaven 2003 ya sake neman wannan kujera kuma Allah ya ba shi, kuma hakan ya zama sanadin zaman shi shugaban Majalisar Wakilai ta Tarayya, wanda shi ne babban muqamin siyasa na farko da jihar Katsina ta samu a tarihin siyasar Nijeriya.

Bayan wancan muqami da ya riqe na shugabancin Majalisar Wakilai ta Tarayya, ya kuma gama shi lafiya duk da karan-tsayen da Shugaba Obasanjo ya riqa yi wa majalisa a baya, ya dawo ya nemi Gwamnan Katsina kuma ya samu goyon bayan jama’ar Jihar Katsina a 2007, amma Allah bai ba shi ba.

 

Watakila saboda qarfin imani ya sanya ya sake dawowa a 2011, A nan xin ma bai samu ba kuma ya haqura ya mayar da al’amarinsa ga Allah. Ya sake dawowa a 2015 kuma Allah ya qwato mulkin Jihar Katsina ya miqa masa.
Waxannan abubuwa da Allah ya xora shi a kai suna da matuqar bukatar nazari. Da farko dukkansu ayyuka ne da suka shafi jagorancin harkokin al’umma. Allah yana bayar da shugabancin jama’a ne ga mutane masu nagarta domin su kai al’umma ga tudun mun -tsira musamman idan yana son su samu kyakkyawan sakamaako a lokacin da suka koma gare shi. Wasu kuma sai a ba su mulkin amma kuma ya zama fitina gare su, musamman idan suka kasance masu girman kai da xagawa a cikin al’ummominsu.

 

 

Alh. Aminu Bello Masari ba ya da tsoron fuskantar duk wani qalubale da ya tunkare shi, musamman idan akwai gaskiya a ciki kuma zai amfani jama’a.

 

Alal misali a lokacin da wasu ‘yan siyasa suka qulla makircin ta-zarcen Shugaba Obasanjo a 2007, an kawo batun gaban majalisar wakilai domin amincewarta, amma ya fito fili ya bayyana cewa hakan ya savawa tsarin mulki kuma majalisa ba za ta savawa tsarin mulki ba. Daga nan maganar ta wargaje.

 

Ina so in tuna maku cewa wancan mataki da ya xauka ya ceto Nijeriya da tsarin dimokiraxiyya daga wargajewa. Ba domin wancan mataki ba da babu dimokiraxiyya a Nijeriya a yau, watakila ita kanta Nijeriyar da ta zama tarihi.
Watakila da yana da tsoro ko rauu, ba zai iya xaukar wancan mataki ba, musamman ganin cewa jam’iyyarsa, wato PDP ce ta qulla makircin Shugaba Obasanjo ya zarce. Haka kuma barazanar tsige shi da wasu abokan aikinsa suka fara qoqarin yi bai razana shi ba. An kafa tarkunan da za a kama shi da wani laifi domin a ci masa mutunci, amma duk suka gaza kama shi.

 

A lokacin da ya fito neman gwamnan Jihar Katsina a 2007 babu wani xan takara da ya kai shi magoya baya, amma aka yi amfani da qarfin iko aka karya lagonsa. A haka ya rungumi qaddara ya saurari zuwan 2011. Duk da cewa ya fice daga PDP suka sake bin shi inda ya koma, suka sake sukurkuta tsari da burinsa na zama gwamnan Jihar Katsina. Wannan bai sanya ya karaya ba. Ya sake dawowa a 2015 ya sake neman wannan kujera, abin ya zo daidai da yadda Allah ya tsara, ya lashe zaven gwamnan Jihar Katsina. A halin yanzu yana kan wa’adi na biyu kuma na qarhe akan wannan kujera. Muna yi ma shi fatar ya kammala wannan wa’adin cikin nasara.

 

 

Ba mu da nufin tuna maku mashahuran ‘ya’yan Jihar Katsina da suka bayar da gagarumar gudunmuwa ga gina Nijeriya,, amma hakan ya zama wajibi domin ilimintar da waxanda ba su sani ba ko kuma suka manta.
Daga cikin wannan rukuni akwai Marigayi Janar Shehu Musa ‘Yar’aduwa. A lokacin da gwamnatin Janar Babangida ta buxe fagen siyasa domin mayar da mulki hannun farar hula, Janar Shehu Musa ‘Yar’aduwa ya bayyana a farfajiyar siyasar Nijeriya. A tarihin Nijeriya babu wani mutum xaya da ya shahara kuma kuwwarsa ta kai kowane lungu da saqo na Nijeriya kamarsa. Babu wani saqo da lungu, babu wata qabila, babu wani mabiyin addinin da bai ji sunan Janar ‘Yar’aduwa ba a zamaninsa.

 

 

Hasali ma ya yi qarfin siyasar da babu wani xan siyasar da ya taba yi a Nijeriya.
Kafin Janar ‘Yar’aduwa an yi su Janar Hassan Usman Katsina, tsohon Gwamnan Jihar Arewa wadda ta qunshi jihohin arewa 19 da Birnin Abuja, kuma tsohon Hafsan Sojan Nijeriya kuma yana cikin mutanen da suka sadaukar da rayukansu wajen ganin Nijeriya ta xore a matsayin qasa xaya.

 

Sa’annan ga Alhaji M D Yusuf, tsohon Sufeto Janar na ‘Yansandan Nijeriya kuma tsohon xan takarar shugaban qasa a tsohuwar jam’iyyar GDM da MDJ,

 

Sa’annan akwai Marigayi Ibrahim Commassie, wanda ya shiga aikin xan sanda har ya kai muqamin Sufeto Janar.

 

Ga kuma tsohon shugaban qasa Marigayi Alhaji Ummaru Musa ‘Yar’aduwa wanda ya yi gwamna kuma ya yi shugaban qasa.
A yanzu ga Shugaba Muhammadu Buhari, wanda sai da ya kai qololuwa a harkar aikin soja, ya zama shugaban gwamnatin mulkin soja, ya sake dawo wa cikin harkokin siyasa har ya zama shugaban qasa.

 

 

Akwai sauran mashahuran Katsinawa da suka taka muhimmiyar rawa a harkokin inganta rayuwar jama’a waxanda rashin wadatar fili da lokaci ba za su ba mu damar kawo su ba.

Muna son Alh. Aminu Bello Masari ya dubi baya ya dubi gaba ya dubu Nijeriya da al’ummarta. Ya dubi irin halin da Nijeriya da ‘yan Nijeriya ke ciki a fannin tsaro da tattalin arziki da zamantakewa. Muna bukatar ya shiga cikin harkokin shugabancin Nijeriya saboda ya san abubuwa da yawa da akasarin ‘yan Nijeriya ba su sani ba. ya san ‘yan siyasar Nijeriya daga vangarori daban daban, daga mabiya addini dabam daban, ya san harkokin zartaswa da harkokin majalisa.

 

Hasali ma Allah ya ba shi lafiya da qarfin zuciyar tunkarar abubuwa ta hanyoyin da suka dace, yana da qoqarin neman shawara da amfani da shawarar da jama’a suka ba shi domin samun mafita.

Wannan ya sanya mutane, na kusa da na nesa da mazavarshi sun riqa bayar da goyon bayansu gareshi domin sun yi itifaqin cewa jari ne suke zubawa domin irin wannan lokaci da Nijeriya ta samu kanta a ciki.

 

 

Akan haka muke ganin bai kamata ya janye jiki daga harkokin siyasar Nijeriya ba, musamman ganin inda muka ratso da kuma halin da ake ciki. Akwai bukatar ya koma Majalisar Dattijai domin ci gaba da bayar da gudunmuwar da ta dace domin abubuwa su inganta. Sa’annan kasancewar mutane irinsa a majalisar zai sanya ta daidaitu ta yadda za ta riqa taka rawar da ta kamata ta taka kuma a hankali suna koyawa na baya abubuwan da suka dace a riqa yi domin abubuwa su inganta.

 

 

Alh. Aminu ya zama kayan jama’a kuma watakila wasu daga cikin abubuwan da jama’a za su bukaci ya yi ba za su yi ma shi daxi ba, AMMA KUMA ZA SU YI WA JAMA’A AMFANI.

Idan muka bari wannan dama ta wuce mu, to gaskiya Jihar Katsina da sauran ‘yan Nijeriya za mu yi babbar hasara da baqin ciki.

 

 

La’akari da waxannan abubuwa ya sanya muke kira ga Mai Girma Alh. Aminu Bello Masari da ya canza waccan shawara, ya dawo da’irar siyasa a ci gaba da gudanar da kyakkyawan aikin da ake yi, ya tafi Majalisar Dattijai ta Nijeriya a zaven 2023.

Haka kuma muna roqon manya da shugabannin Jihar Katsina, musamman Mai Martaba Sarkin Katsina, Dokta Abdulmumini Kabir Usman da Mai Martaba Sarkin Daura, Alh. Farouk Umar Farouk da malamai da sauran jama’a su taya mu kira ga Alhaji Aminu Bello Masari domin duba wannan al’amari,

 

 

Mohammad Lawal Maikuxi
Kakakin Gamayyar Qungiyoyin Kishin Kasa,
JiharKatsina
08037033258

About andiya

Check Also

KADCCIMA ON  ON REVIEW OF ELECTRICITY TARIFF

    Following approval by the Electricity Regulatory Commission (NERC) for the increase of electricity …

Leave a Reply

Your email address will not be published.