Home / Labarai / Gwamna Masari Ya Mayar Da Dokar Hawan Babur Karfe 11 Na Dare

Gwamna Masari Ya Mayar Da Dokar Hawan Babur Karfe 11 Na Dare

Gwamna Masari Ya Mayar Da Dokar Hawan Babur Karfe 11 Na Dare
Mustapha Imrana Andullahi
Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana cewa Biyo bayan sauraren koke koken al’umma tare kuma da yin la’akari da ci gaban da ake samu a bangaren tsaro, da yammacin yau Talata da karfe (6:30pm), Gwamna Aminu Bello Masari ya sanya hannu a kan dokar da tayi gyara a kan dokar takaita zirgazirgar Babura a cikin jihar Katsina.
Sakamakon wannan gyara, daga yau, 1 ga watan Satumba na shekarar 2020, dokar takaita zirgazirgar baburan za ta fara aiki ne da karfe Goma sha daya (11:00pm) na daren kowace rana. Sauran duk bayanin da dokar ke dauke dashi tun da farko yana nan yadda yake.
Ke nan, masu babura za suci gaba da hidimar su har zuwa karfe 11:00 daren kowace rana.
Ana kira ga al’umma su kiyaye, su kuma jami’an tsaro suyi la’akari da wannan gyara kuma su kiyaye.
A kwanakin bayyane saboda irin yadda harkokin tsaro suka shiga cikin wani mawuyacin hali inda Gwamnati ta fahimci cewa wadansu yan bindiga da masu Garkuwa da Mutane da sauran batagari suna yin amfani da Babura wajen aikata mugun aikin nasu yasa Gwamnatin ta Sanya dokar hana yin amfani da Babura da misalin karfe 6 na Yamma zuwa wayewar gari domin takaita ayyukan na batagari.

About andiya

Check Also

Tinubu Appoints Silas Ali Agara DG NDE

By Ibraheem Hamza Muhammad President Bola Ahmed Tinubu has approved the appointment of Honourable Silas …

Leave a Reply

Your email address will not be published.