Related Articles
Daga Imrana Abdullahi
Gwamna Dikko Umar Radda ne ya aza harsashin ginin cibiyar kula da lafiya ta duniya a babban asibitin Janar Amadi Rimi da ke yankin karamar hukumar Batagarawa a jihar.
Kakakin Malam Dikko Radda, Ibrahim Kaula Mohammed, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce taron na daga cikin ayyukan da aka tsara domin tunawa da cika kwanaki 100 da ya yi a kan karagar mulki a matsayin gwamnan jihar Katsina.
Kwamishinan lafiya na jihar Dokta Bishir Gambo Saulawa ya bayyanawa manema labarai yadda aikin yake gudana a wani taron tattaunawar da suka yi da shi.
Ya ce Cibiyar wankin Kodar, idan aka kammala ta, za ta kasance daya daga cikin mafi kyau a Arewacin Najeriya. Ya ce za a kafa irin wannan cibiyar kiwon lafiya a garin Funtua don kula da marasa lafiya da ke buƙatar aikin wankin Kodar.
“Tun da dadewa, kuma kafin yanzu, Jahar mu mai kauna tana da injinan wankin Kodar guda hudu a babban asibitin Katsina.
“Ya zuwa lokacin da aka kammala sabbin Cibiyoyin kula da Lafiyar Jiki guda biyu, za mu kasance da na’urorin wankin Kodar guda 16,” in ji shi.