Home / Ilimi / Gwamna Radda Ya Nada Sabon Shugaba, Sakatare, Membobin Hukumar Malamai ta Katsina

Gwamna Radda Ya Nada Sabon Shugaba, Sakatare, Membobin Hukumar Malamai ta Katsina

Daga Imrana Abdullahi

Gwamna Dikko Umaru Radda ya amince da nadin Alh.  Sada Ibrahim a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Ayyukan Malamai ta Jihar Katsina, (Teachers Service Board).

Wata sanarwa da Ibrahim Kaula Mohammed, mai magana da yawunsa ya fitar ta bayyana cewa Radda ya kuma amince da nadin wasu mutane biyar a matsayin Sakatare da Mamba na dindindin a hukumar.

Sun hada da; Honarabul Usman Umar Yaba a matsayin mamba na dindindin, Alhaji Mannir Yahaya a matsayin mamba, Alhaji Usman Umar Mai’adua a matsayin mamba, Hajiya Uwani kafin Dangi a matsayin mamba, sai Alhaji Umar Lawal a matsayin sakatare.

Nadin nasu ya fara aiki daga ranar Litinin, 21 ga Agusta, 2023.

Alhaji Sada Ibrahim ya fito ne daga karamar hukumar Dutsin-ma kuma ya yi karatun Digiri na farko, B.A (Ed) a harshen Ingilishi daga babbar jami’ar Ahmadu Bello (ABU) Zariya a shekarar 1996.

Har zuwa nadin nasa na baya-bayan nan, ya kasance mataimakin darakta a hedikwatar NYSC ta kasa, Abuja, inda ya yi aiki sama da shekaru 28 a jami’o’i daban-daban.

About andiya

Check Also

Return Our Property, Documents In Your Possession, SWAN Tells Ex-President Sirawo

    The Sports Writers Association of Nigeria (SWAN) has warned its erstwhile National President, …

Leave a Reply

Your email address will not be published.