Daga Abdullahi Muhammad
Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya nada Malam Abdullahi Sarkin Danko a matsayin babban sakatare a Gwamnatin Iihar.
Kafin Nadine nasa Danko shi ne babban mataimaki ne na musamman ga Gwamnan a kan harkokin kafafen yada labarai da yayata al’amuran yau da kullum.
Wannan na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun babban mai ba Gwamnan Tambuwal shawara kan kafin yada labarai Muhammad Bello.
An kuma nada Hajiya Amina Muhammad Jekada, wadda ta kasance a yanzu ita ce Darakta Janar na wurin shakatawar Jihar.
This was contained in a press statement signed by Muhammad Bello special adviser, media and publicity to the Governor.
Sauran da aka nada sun hada da Alhaji Bandado shehu Bandi, shugaban sashin Zane Zane na kwalejin ilimi ta Sakkwato, da Husaini S. Gobir matsayin darakta a hukumar kula da ilimin jihar.
Kamar yadda takardar ta fito daga Gwamnatin Jiha, mutanen hudu an muna cancantarsu ne domin a ba su wadannan mukamai saboda yadda guraben aikin suka kasance ba kowa kuma suna bukatar a cike su domin aikin Gwamnati ya gudana kamar yadda ya dace”.
“An kuma ba su wadannan mukamai ne saboda karon aikin su don haka aka ga cancantarsu a matsayin manya sakatarorin Jihar, takardar da samu sa hannun shugaban ma’aikatan Jihar Dakta Buhari Bello Kware”.
Shi dai Danko ya samu takardar digirinsa ne a shekarar 1995 saga Jami’ar Usman Danfodiyo da ke Sakkwato a kan ilimi da tarihi inda ya zama darakta daga matsayin mai kawo rahoto a can farko.
Shi kuma Jakada, ya samu shaidar digirinsa ne a kan kimiyya yanayi daga jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya an kuma dauke shi aiki a matsayin mai aikin tsara birane a shekarar 1992.
Bandi, ma ya fara aiki ne a shekarar 1988 a matsayin mataimakin shugaban da ke kula da sashin ilimi yana da digiri da kuma digirin digirgir a kan harkar zane Zane daga Jami’ar Ahmadu Bello Zariya.
Haka zalika Gobir, da ke da digiri a fannin ilimi ya fara aiki ne daga karamar hukuma a shekarar 1990 ya kuma rike mukamai da dama a makarantu da kuma shugaban sashin tsare tsare.
Duk wadannan nade naden sun fara aiki ne nan take kamar yadda takardar ta bayyana.