Home / Ilimi / Gwamna Uba Sani Ya Cika Alkawari – Abdulrahman Zakariyya Usman

Gwamna Uba Sani Ya Cika Alkawari – Abdulrahman Zakariyya Usman

Daga Imrana Abdullahi

An bayyana Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani a matsayin mutumin da ya cika alkawarin da ya dauka a cikin kasa da kwanaki dari da ya fara jagorancin Jihar Kaduna.

Babban mai ba Gwamna Uba Sani shawara a kan harkokin addini Shaikh dan Shaikh Abdulrahman Zakariyya Usman ne ya bayyana hakan ne a wata tattaunawar da ya yi da gidan rediyon Freedon da ke Kaduna, inda ya ce hakika Gwamnan ya cika alkawarin da ya dauka a lokacin neman a zabe shi Gwamnan Jihar.

“Kun ga ya Sanya murna da farin ciki ga fuskokin dimbin jama’a da suka hada har da wadanda za su yi karatu nan gaba da masu yi a yanzu da kuma jama’ar duniya baki daya”.

“Kun ga dalibai da iyaye da kuma mutanen Jihar duk sun yi farin ciki da murna da wannan batun rage kudin makaranta da aka yi”.

Mai bayar da shawarar ya ce ba a raba bangaren karatun boko da na Islama saboda haka akwai tsare – tsare na musamman a kan hakan da Gwamnan ya yi ta yadda za a samu tafiyar al’amura kamar yadda ya dace musamman a bangaren makarantun Tsangaya.

Shaikh Andulrahman sai ya yi kira ga iyaye da su rika yi wa Gwamnatin da addu’o’i da kuma Sanya idanu a kan yara ta yadda al’amura za su ta fi kamar yadda ya dace.

“Lallai babu shakka akwai shirye shirye domin a yanzu kun fara gani a bangaren abin da ya shafi biyan kudin manyan makarantu, saboda haka ne muke yin kira tare da fadakarwa ga iyaye a kan bukatun da ke akwai na Sanya idanu a kan yayansu danga ne da abin da ke faruwa a cikin kwanakin nan kuma ya dace a yawaita bin su da addu’o’i, a irin wannan yanayin da muke ciki domin kada ya zamanto ana yin kitso da kwarkwata ya zamanto Gwamnati na kokari amma kuma su iyaye ba su kulawa da Sanya idanu  ga dukkan al’amuran yayansu da abin da suke aiwatarwa a yau da kullum, sannan kuma su dinga bin yayan da addu’a tare da fatan Allah ya yi masu albarka”.

Ya kuma shawarci al’umma da su hada hannu da Gwamnatin Jihar Kaduna da ta kasa baki daya da nufin samun zaman lafiya da hadin kai, “mutane dole ne su hada hannu tare da karfi da karfe da nufin duk wanda ke da ikon fadakarwa ko tsawatarwa ya tsawatar kuma akwai bukatar a hadu a zama tsintsiya madaurinki daya game da abin da ya shafi ci gaba domin a samu abin da ake fatar samu. Ya zama wajibin wajibi mu yi karatun tanatsu sa’annan mu nemi abin da zai zamar mana zaman lafiya da hadin kai ta yadda za a samu ci gaban da ake bukata a koda yaushe”.

About andiya

Check Also

Return Our Property, Documents In Your Possession, SWAN Tells Ex-President Sirawo

    The Sports Writers Association of Nigeria (SWAN) has warned its erstwhile National President, …

Leave a Reply

Your email address will not be published.