Related Articles
Gwamna Zulum Da Sauran Jama’a Sun Yi Sallar Jana’izar Shehun Dikwa A Maiduguri
Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, Shehun Borno, Abubakar Umar Garbai El- Kanemi, da sauran Sarakunan Gargajiya da kuma manya manyan jami’an Gwamnati na cikin dimbin mutanen da suka halarci Sallar Jana’izar marigayi Shehun Dikwa, Mohammed Ibn Masta II.
Limamin Borno Liman Idaini, Shetima Mamman Saleh ne ya jagoranci Sallar a fadar Shehu Borno da ke garin Maiduguri.
Shehu Mohammed Ibn Masta na biyu ya rasu ne a Abuja a ranar Asabar yana da shekara 75, bayan fama da rashin lafiya.
Gwamnan da yake ganawa da manema labarai bayan an kammala Sallar ya bayyana rashin da cewa abu ne mai sa kaduwa kuma rashi ne babba da ya bar wani gurbi mai wuyar cikewa.
“Hakika wannan yanayin bakin ciki ne ga al’ummar Jihar Borno da masarautar Dikwa. Marigayin abin ko yi ne, mutum ne mai natsuwa , kuma mutum ne mai tausayi kwarai. Don haka zamu yi rashinsa kwarai muna addu’a ga Allah madaukakin Sarki ya jikansa ya sa Aljannah makomarsa”, inji Zulum.
“Mutuwar ta girgizamu domin shi ne jigo a masarautar Dikwa. Don haka rashinsa ya bar wani gurbi mai wuyar cikewa. Saboda haka ne muka yanke hukuncin Dakatar da dukkan abin da zamu yi a yankin Kudancin Jihar Borno domin mun rasa Sarki. Shi yasa muka dawo gida da Sauri mu halarci Sallar Jana’izarsa”.
Shehun Borno, Abubakar Umar Garbai El- Kanemi ya bayyana rashin da cewa babban rashi ne ga daukacin al’ummar Jihar Borno baki daya.
” hakika akwai bakin ciki da kuma tausayawa domin babban rashi ne a garemu Baki daya, a gaskiya yana daga cikin Sarakunan da ake ganin girmansu, domin shi ne wanda yake da mafi girman mukami a jerin sarakunan Jihar Borno.
Bayan ni sai Shehun Dikwa, saboda haka shakka babu an yi babban rashi ba wai ga iyalansa kawai ba ko mutanen Dikwa ba,ga Jihar Borno baki daya Allah ya bashi Aljannah Firdausi”, inji Shehu Garbai.