Home / Ilimi / Gwamna Zulum Ya Bayar  Da Umarnin Daukar Nauyin Dalibai 100 Su Karanta Kimiyyar Kididdigar Gine gine

Gwamna Zulum Ya Bayar  Da Umarnin Daukar Nauyin Dalibai 100 Su Karanta Kimiyyar Kididdigar Gine gine

Gwamna Zulum Ya Bayar  Da Umarnin Daukar Nauyin Dalibai 100 Su Karanta Kimiyyar Kididdiga
Mustapha Imrana Abdullahi
A kokarin ganin Jihar Borno ta ci gaba da samun kwararrun masana a kan harkokin Gine ginen gidaje domin amfanar yan asalin Jihar Gwamna Babagana Umara Zulum ya bayar da umarnin daukar nauyin yan asalin Jihar Borno mutane 100 su karanta kimiyyar kididdigar Gone gine a makarantun kasar nan daban daban.
Gwamna Zulum ya bayar da umarnin ne a ranar Laraba lokacin da yake bude taron kwanaki biyu da cibiyar horar da masu aikin kimiyyar kididdigar Gine gine ta kasa ta shirya, mai taken samun hadin kai domin ci gaba a bangaren masana’antar kerekere.
Gwamna Zulum ya bayar da umarni ga shugabannin kananan hukumomi 27 da ke Jihar borno Borno su hanzarta gabatar mika sunayen yan asalin kananan hukumomin uku domin ci gaba da kokarin zuwa karatun.
“Shugabannin kananan hukumomi 27 da su ssmu cewa an ba su umarnin su gabatar da sunayen Mutanensu uku (3) daga bangaren mutane marasa galihu a cikin al’ummominsu domin Gwamnati ta dauki nauyin karatun na su”, inji Zulum.
Wannan amincewar da Gwamna Zulum ya bayar zai iya taimakawa domin samun maganin karancin masu irin  wannan aikin da kuma bukatar masu kididdigar Gine gine a Jihar Borno. An dai tabbatar da cewa Jihar Borno na da masu kimiyyar kididdigar gine gine mutum Tara ne kawai, wanda bisa la’akari da bukatun da ake da su a Jihar hakika sun yi karanci saboda aikin gine gine da gyare gyaren da ake yi a duk fadin Jihar a halin yanzu.
“Lokacin da na karbi bakuncin shugaban wannan cibiya jiya a ofishinsa, nan ne na san cewa muna da masu aikin kimiyyar kididdigar Gine gine guda Tara (9) ne kawai a Jihar Borno. Don haka ba za mu bari irin wannan al’amari ya ci gaba ba”, inji shi.
A jawabinsa shugaban cibiyar Mohammed Abba Tor cewa ya yi, zabin da suka yi wa Juhar Borno don gudanar da wannan taron sakamakon irin yadda ake hidintawa al’ummar kasa baki daya da Gwamnatin da Zulum yake yi wa shugabanci a tsawon shekaru biyu.
Shugaban cibiyar ya kuma bayyana farin cikinsa da samun gamsassun bayanan irin abin da Gwamnan ke yi inda ya kara da yi masa godiya ga Gwamna Babagan Umara Zulum bisa daukar nauyin wannan babban taron na cibiyar da aka yi a dakin taro na gidan Gwamnatin Jihar Borno wanda ya ce wannan shi ne tarihin cibiyar na farko a samu irin wannan karramawar da aka yi wa cibiyar tare da yayanta baki daya.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.