Home / Labarai / Gwamna Zulum Ya Dora Harsashin Ginin Tasha, Shaguna 593 Da Kasuwa Kan Kudi Naira Biliyan 2

Gwamna Zulum Ya Dora Harsashin Ginin Tasha, Shaguna 593 Da Kasuwa Kan Kudi Naira Biliyan 2

Gwamna Zulum Ya Dora Harsashin Ginin Tasha, Shaguna 593 Da Kasuwa Kan Kudi Naira Biliyan 2
Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya Dora Harsashin ginin  sabuwar Tashar Mota, shaguna dari 593 da kuma kasuwa irin na zamani dukkansu a kan kudi naira biliyan biyu.
A wurin da za a gina kasuwar na da Filin mai fadin mita dubu 49 ya na a kan titin zuwa Bama ne cikin Maiduguri, da zai kunshi shaguna 373 wurin kasuwanci 220 da ya hada shaguna 593 dai-dai.
Gwamna Zulum ya kuma bayyana cewa wannan aikin ana saran kammala shi ne a cikin watanni 18 masu zuwa, sai ya yi kira ga yan kwangilar da su yi aiki a cikin lokacin da aka kayyade masu tare da yin mai inganci.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa sabon wurin da ake ginawa zai bayar da damar a mayar da Tashar mota ta titin Bama zuwa babban sabon wurin idan an kammalashi, za kuma a kafa babbar makaranta a wurin da tashar za ta tashi duk domin amfanin jama’a.
Kwamishinan ciniki da masana’antu Yerima Kareto,ya ce an bayar da aikin ne ga yan kwangila Goma kuma tuni aka ba su kashi Goma sha biyar na kudin.
Da yake jawabi a madadin wadanda za su yi aikin, Injiniya Usman Tijjani Monguno bayar da tabbaci ya yi cewa za a tabbatar da yin aikin mai inganci kamar yadda aka tsara aiki a tsare tun farko.

About andiya

Check Also

Tinubu Appoints Silas Ali Agara DG NDE

By Ibraheem Hamza Muhammad President Bola Ahmed Tinubu has approved the appointment of Honourable Silas …

Leave a Reply

Your email address will not be published.