Home / Labarai / Gwamna Zulum Ya Ziyarci Hukumar Raba Dai-dai Ta Kasa

Gwamna Zulum Ya Ziyarci Hukumar Raba Dai-dai Ta Kasa

Gwamna Zulum Ya Ziyarci Hukumar Raba Dai-dai Ta Kasa
Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Borno Banagana Umara Zullum ya kai ziyara hukumar raba dai-dai ta kasa inda ya bukaci hukumar ta bayar da muhimmanci ga yan asalin Jihar wajen daukar aiki.
Gwamna Farfesa Banagana Umara Zullum lokacin da ya kai ziyara hedikwatar hukumar raba dai-dai ta kasa a Abuja ranar Litinin, inda nan take ya bukaci hukumar da ta bayar da muhimmanci ga Jiharsa a duk lokacin da za a dauki aiki a Nijeriya.
Zullum, ya samu gagarumar tarba daga shugaban hukumar da kuma Sakataren hukumar Dokta Muheeba F. Dankaka da Mohammed Bello Tukur.
Gwamnan ya bayyana cewa sakamakon irin illar da Jihar ta samu saboda matsalar Boko Haram, Dubban daruruwan mutanen Jihar sun rasa hanyoyin cin abincinsu na rayuwa da akwai kuma wadansu matasa da yawa ba su da aikin yi duk da kokarin da Jihar ke yi wajen samawa jama’a abin yi a kullum ta hanyoyi daban daban.
Gwamna Zulum ya ce hakika bayar da kulawa ta musamman ga al’ummar Jihar Borno a wajen daukar aiki zai taimakawa kasa baki daya musamman ganin irin yadda lamarin aikin Hwamnatin tarayya yake.
Gwamnan wanda shi ne shugaban kungiyar Gwamnonin yankin Arewa maso Gabas ya kuma yi kira ga daukacin Jihohi da su bayar da kulawa ta musamman ga yankin fiye da sauran wurare a tarayyar Nijeriya, duk da Jihar Borno ta samu matsala sakamakon rikicin Boko Haram, suma sauran yankunan da ke Jihohin yankin duk sun samu matsala kwarai sakamakon hakan saboda hakan duk sun cancanci samun kulawa ta musamman daga Gwamnatin tarayya musamman wajen daukar matasa aiki.
Shugabar hukumar raba dai-dai Dokta Muheeba F. Dankaka ta yi alkawarin duba wannan bukata da Gwamna Zullum ya gabatar wa hukumar, inda ta tabbatar da cewa halin da Jihar Borno ke ciki abu ne sananne ha kowa, don haka za a yi wa Jihar Borno adalci a wajen rabon guraben aikin da za a samar.
Shugabar hukumar wadda take tare da daukacin kwamishinonin hukumar da ke wakiltar Jihohin Nijeriya, duk sun godewa Gwamna Zullum bisa irin kokarin da yake yi domin ganin rayuwar jama’a ta inganta a koda yaushe.
Wadanda suke a cikin tawagar Gwamna Zullum sun hada da shugaban ma’aikatan gidan Gwamnatin Jihar, Farfesa Isa Hussaini Marte, da wasu daga cikin Kwamishinoni, da kuma wasu al’ummar Jihar Borno duk sun je wurin domin taimakawa kiran da Gwamna Zullum ya yi domin rayuwar mutanen Jihar ta inganta.

About andiya

Check Also

Majalisa Ce Ta Bambanta Dimokuradiyya Da Mulkin Karfa Karfa – Ado Doguwa

  …Sai An Ba Kananan hukumomi Yancinsu   Bashir Bello majalisar Abuja Honarabul Alhassan Ado …

Leave a Reply

Your email address will not be published.