Related Articles
Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Bauchi Bala Muhammed da sanannen Attajiri Alhaji Aliko Dan gote sun tattauna kan batutuwan zuba jari da inganta harkokin lafiya a Jihar Bauchi.
An dai samu damar wannan tattaunawar ne a lokacin wata ziyara wadda ta samu nasara da Gwamnan Bauchi ya kai Ofishin sanannen dan kasuwar.
Dangote dai ya bayar da taimakon kudi naira miliyan dari biyu domin bayar da taimako ga mata masu kokarin sana’a a Jihar.
Dangote ya bayar da tallafin ne ga mata masu fuskantar barazanar talauci a Jihar Bauchi ta yadda rayuwarsu za ta inganta.
Dan kasuwar ya Kuma yi alkawarin gina kananan Asibitoci biyar (5) a jihar Bauchi duk domin taimako wajen inganta rayuwar al’ummar Jihar baki daya.