Home / Lafiya / Gwamnan Bauchi Da Dangote Sun Tattauna Batutuwan Zuba Jari Da Tattalin Arziki

Gwamnan Bauchi Da Dangote Sun Tattauna Batutuwan Zuba Jari Da Tattalin Arziki

Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Bauchi Bala Muhammed da sanannen Attajiri Alhaji Aliko Dan gote sun tattauna kan batutuwan zuba jari da inganta harkokin lafiya a Jihar Bauchi.
An dai samu damar wannan tattaunawar ne a lokacin wata ziyara wadda ta samu nasara da Gwamnan Bauchi ya kai Ofishin sanannen dan kasuwar.
Gwamnan Jihar Bauchi tare da Tawagarsa lokacin da suka kai ziyara ofishin Dangote domin karfafa zumunci9
Dangote dai ya bayar da taimakon kudi naira miliyan dari biyu domin bayar da taimako ga mata masu kokarin sana’a a Jihar.
Dangote ya bayar da tallafin ne ga mata masu fuskantar barazanar talauci a Jihar Bauchi ta yadda rayuwarsu za ta inganta.
A dama Alhaji Aliko Dangote tare da Gwamnan Jihar Bauchi Alhaji Bala Muhammed lokacin da suka kai masa ziyara a ofishinsa
Dan kasuwar ya  Kuma yi alkawarin gina kananan Asibitoci biyar (5) a jihar Bauchi duk domin taimako wajen inganta rayuwar al’ummar Jihar baki daya.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.