Home / Labarai / Da dumi Duminsa: An Tabbatar Wanda Ake Zargi Da Cutar Coronavirus A Katsina Bashi Dauke Da Cutar

Da dumi Duminsa: An Tabbatar Wanda Ake Zargi Da Cutar Coronavirus A Katsina Bashi Dauke Da Cutar

Mustapha Imrana Abdullahi

Rahotannin da muke samu daga Jihar Katsina na cewa mutumin da ake zargi da yana dauke da cutar Daukewar Lumfashi da ake kira Corona virus ko Covid 19.

Kwamishinan kula da harkokin lafiya na Jihar Katsina Injiniya Nuhu Yakubu Danja ne ya tabbatar wa da kafar yada labarai ta Katsina Pist haman a ofishinsa.

Da wakilinmu ya tuntubi kwamishinan lafiya na Jihar Katsina Injiniya Nuhu Yakubu Danja ya shaida ma wakilinmu cewa dama ita cutar corona virus na da wadansu Alamomi masu kamanceceniya da Alamomin wadansu cututtuka amma bayan an kammala bincike irin na Gwaje gwaje aka tabbatar cewa wanda ake zargin baya dauke da cutar, don haka ba ita bace.

Ki biyo mu domin kawo maku cikakken bayanin nan gaba kadan…

About andiya

Check Also

GWAMNA DAUDA LAWAL YA HARAMTA HAƘAR MA’DINAI BA BISA ƘA’IDA BA

…YA UMURCI JAMI’AN TSARO SU ƊAUKI TSATTSAURAN MATAKI Daga Imrana Abdullahi A yau Asabar, Gwamnan …

Leave a Reply

Your email address will not be published.