Home / Labarai / Gwamnan Bauchi Zai Ba NASENI Fili Domin Bunkasa Kimiyya Da Fasaha

Gwamnan Bauchi Zai Ba NASENI Fili Domin Bunkasa Kimiyya Da Fasaha

Gwamnan Bauchi Zai Ba NASENI Fili Domin Bunkasa Kimiyya Da Fasaha
Mustapha Imrana Abdullahi
….kasancewar hukumar NASENI a kan gaba wajen bunkasa fannin kimiyya da fasaha 
Gwamna Bala Muhammad Abdulkadir na jihar Bauchi ya bayyana cewa Gwamnatinsa  za ta Samar da fili Mai fadin  hekta 20, hahukumar da ke aikin bunkasa harkokin kimiyya da fasaha ta kasa   “National Agency for Science and Engineering Infrastructure”(NASENI) don inganta aikin su a jihar.
Gwamnan yabayanna hakane a lokacin da mataimakin Shugaban Hukumar, Professor Muhammad Sani Haruna yakawo Masa ziyarar a dakin taro na Majalisar zartarwa dake cikin Gidan Gwamnatin jihar Bauchi.
Gwamna Bala Muhammad Abdulkadir yace da wuri zamu mika musu wannnan fili don fara wannan aiki don susamu sufara kawo aihin inginansu manya don habbaka da inganta jihar a wannan fanni.
Yace Gwamnatinsa zatayi aiki da irin wadannan hukumomi don ta tabbatar da inganta harkan kimiya da fasaha don samun ingantaccen Nasara da cigaban jihar.
Yace sabbin dabarbaru da kirkire kirkire su zasu kawo wa jihar cigaba muna cike da farin ciki sannan zamu Baku dukkan dama a hukumance don kutaimaka mana a Gwamnatance al’ummah su anfana daga gareku.
” A yau ba ranace ta kimiya ba, Amma mu a jihar Bauchi min yarda yau ranace ta kimiya da fasaha, lura da yadda kukazo jihar Bauchi don inganta ta da cigaba, Ina cike da murna a madadin al’ummar jihar Bauchi da Gwamnati mun karbeku hanun biyu biyu na wannan ziyara.
Ina murna matuka da alaka daku don habaka da inganta cigaba musamman Kan yadda zaku Samar mana da yadda za’asamu wuta Mai anfani da hasken Rana.
Gwamna Bala Muhammad yabayyana cewa Gwamnati zata yi nasarane kawai in tasamu irin wadannan ayyuka na cigaba da habaka, yace Gwamnatin jihar Bauchi zata saka kimiya da fasaha agaba wajen habaka sashen da duk sauran fanoni don habaka tattalin arziki.
Mataimakin Shugaban Hukumar,forofeso Muhammad Sani Haruna a lokacin da ke bayyana irin sabbin kudirori dasuke dashi daga Hukumar, yace wannan ziyara munzo ne don musamu aihin goyon baya da taimako wajen aiwatar da wannan aiki da tsare-tsare a jihar.
Forofeso Sani Haruna yace ayanzu haka, jihar Bauchi an zabeta a jihar dazasu anfana daga aihin sabbin ayyuka na kirkira dabarbaru Kan kimiya da fasaha ya bukaci hubbasa da zimma daga Gwamnatin jihar Bauchi don samun ingantaccen Nasara kan Wannan aiki.

About andiya

Check Also

Edo 2024: Group Hold Symposium In Support Of Asue Ighodalo

  The Good Governance Advocacy Group, has held a symposium to drum their support for …

Leave a Reply

Your email address will not be published.