Home / Labarai / GWAMNAN BAUCHI ZAI BADA AIKIN SABBIN TITUNA A KARAMAR HUKUMAR TORO.

GWAMNAN BAUCHI ZAI BADA AIKIN SABBIN TITUNA A KARAMAR HUKUMAR TORO.

GWAMNAN BAUCHI ZAI BADA AIKIN SABBIN TITUNA A KARAMAR HUKUMAR TORO.

 

 

Gwamna Bala Muhammad Abdulkadir na jihar yabayanna kudirin Gwamnatinsa na bada ayyukan hanyoyi a karamar Hukumar Toro Wadda yatashi daga Gumau -Rishi-Tulu-Tama don samun aihin ingantaccen cigaba a wadannan yankuna.

 

Gwamnan yabayanna hakane a lokacin da yakai ziyarar duba aikin hanyar daya tashi daga Maraban Ganye zuwa Gwalpada a cigaba da ziyarar duba ayyukan da akeyi a ciki da wajen jiha.

 

 

Gwamna Bala Muhammad Abdulkadir yabayanna aihin shirin Gwamnatinsa na bada sabbin tituna a wasu garuruwa dasuke Karamar Hukuma don bude’ ta bunkasa musamman harkokin kasuwanci da yalwatar arxiki a wadannan wajaje.

 

Gwamnan yace hanyar daya tashi daga Maraban Ganye wadda aihi Gwamnatin data gabata ne tabada aikin Kan farashi samada Biliyan Daya da dari Shida, Amma damukazo muka aihin sake dubawa da kwararru, ansamu aihin sauki na aiki da wajen Miliyan 120 a cikin kudin da aka ware a baya karakshin Gwamnatinsa.

 

 

Yace yanzu haka Gwamnatin jiha tabasu Miliyan 800 don suci gaba da aiki wadda a yanxu yakai Kashi 75% na kammalawa wadda yace za’a karasa musu don su karasa.

 

 

Kamar yadda kuka sani wannan aiki Gwamnatin data shude’ ita tabada aikin, Gwamnatina ta yanke Shawaran taci gaba da aikin don al’ummar wadannan yankuna sun anfana.

 

 

Ina Kara Tabbatar muku dacewa Gwamnatina bazata bar duk wani aiki ba da akayi watsi dashi ba lura da cewa al’umma ne zasu amfana.

 

Gwamntinmu zata bi dukkan ayyuka da tagada wadda akayi watsi dashi don a cigaba don al’umma jiha su anfana.

 

 

Gwamna Bala Muhammad Abdulkadir yace Wannan aikin hanya wadda yatashi daga Maraban Ganye zuwa Gwalpada, in angama shi zai bada dama bunkasa tattalin arxiki da kasuwanci lura da irin albarkatun noma dake yankin kamar Dankalin Hausa, Tumatur, Albasa, da sauran kayan Miya.

 

 

Gwamnan bude wasu ayyuka a Babban Asibitin Karamar Hukumar Toro, yace Gwamnatinsa zata cigaba da hadin gwiwa da (NSHIP) wadda angina da Gyara samada Asibiti 190 don tabbatar dasamun aihin ingantaccen aiki a Asibitotinmu.

 

A lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai Bayan duba aikin ruwa a Gubi Dam, Maigirma Gwamna Bala Muhammad yabayyana jindadinsa yadda yace in angama wannan na fadada matatar ruwan zai kawo karshen karancin ruwa da ake fama dashi a cikin Garin Bauchi.

 

Ayyukan da Gwamna Bala Muhammad ya ziyarta yahada da Aikin hanyar Maraban Ganye zuwa Gwalpada, Gyaran Babban Asibitin Toro, karamar Asibiti a Magama Gumau, Rimin Zayam, da aikin Hutan lantarki a Garin Mai Allo, Gyara da Sabunta Gidan Hakimin Nabardo, Karamin Asibitin Nabardo, da Babban tankin ajiyar Ruwa dake Miri, Karamin Asibitin dake tashan durmi, da Wajen tura ruwa da aka gina a jikin Makarantan (ATAP.)

Sauran sun hada’ da Tankin Ruwa na buzaye, Aikin Titin Gubi Dam, Aikin saka sabbin injina na zamani a cikin Gubi Dam, Sabbin Gidajen Ma’aikatan Water board, da Aikin Gina tituna a daga Muda Lawal – Bakin Kura- Malam Goje.

 

About andiya

Check Also

An Bukaci Yayan Jam’iyyar APC Da Su Ci Gaba Da Zama Tsintsiya Madaurinki Daya

….Lukman Ya Daina Surutu, A bari Majalisa ta yi aikin ta Daga Imrana Abdullahi Shugaban …

Leave a Reply

Your email address will not be published.