Home / Labarai / Gwamnan Yobe Ya Kaddamar Da Kayan Tallafin Sanata Gaidam Ya Samawa Jama’arsa

Gwamnan Yobe Ya Kaddamar Da Kayan Tallafin Sanata Gaidam Ya Samawa Jama’arsa

Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu

Gwamna Mai Mala Buni na jihar yobe, ya kaddamar da rabon kayayyakin tallafi a hukumance wanda Sanata mai wakiltar Yobe ta Gabas Sanata Alhaji Ibrahim Gaidam ya dauki nauyinsa wadda shi ne shugaban kwamitin majalisar ilimi a matakin farko a majalisar ta Dattawa.

An gudanar da rabon kayayyakin tallafin ne a baban filin wasa na 27 AUGUSTA da ke tsakiyar babban birnin Jihar Damaturu.
Daga cikin kayayyakin da aka raba sun hada da: Injin dinki na 213, kekunan dinki 136 TL3D, Firiza-firiza guda 50 kirar Thermacool deep freezers, sai Snow deep Friza Guda 134 Snow seat deep freezers guda 50,  sai stablizers masu karfin 200watts guda sai injinan markade guda  49 sai Wall dryers gida 30 Wall dryers KLM, 30 KLM sai injinan gyaran gashi guda 188 Pro da  kujerun Saloon 30, Injin lantarki (generators) guda 217 sai kananan  tebura na yara guda  982, da kujeru su kowanne.

Sauran abubuwa sun hada na’urori masu kwakwalwa (Laptopsj)  da jakkunana su guda 5 hade da na’urar buga takardu guda  famfon ruwa ban ruwa guda  15 sai motocin noma Tractors  Samfurin Mercy Ferguson guda 04, sai Wheelbarrow 67, da Litattafan motsa jiki 27,264 bi da bi.

Ana sa ran za a raba kayayyakin a fadin mazabar Sanatan da suka hada da kananan hukumomin Damaturu, Gujba, Gulani, Tarmuwa, Yunusari, Geidam, da  Karamar Hukumar Bursari.

Wasu daga cikin irin kayayyakin da aka raba

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.