Home / Labarai / Gwamnan Zamfara ya gana da Mataimakiyar Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya don taimakawa akan sha’anin tsaro da lafiya.

Gwamnan Zamfara ya gana da Mataimakiyar Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya don taimakawa akan sha’anin tsaro da lafiya.

Mustapha Imrana Abdullahi

 

 

Gwamnan jahar Zamfara Hon Bello Muhammad Mutawalle ya gana da Mataimakiyar Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Amina J Mohammed a garin New York don tattaunawa akan hanyoyin samar da agaji na gaggawa ga jahar Zamfara, mussaman akan lamarin tsaro da bunkasa sha’anin lafiya da ciniki a jaharsa.

 

 

Gwamnan jahar Zamfara wanda tun farko ya amsa gayyata Mataimakiyar Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya don zuwa kasar Amurka ya tattauna da ita a lokacin taron Majalisar Dinkin Duniya dake gudana yanzu haka a garin New York, inda ya samu isa ofishin ta, tare da kwashe lokaci suna tattauna batutuwa da hanyoyin da za abi ga samar da tallafi da agaji ga yan gudun hijira wadanda ayyukan ta’addanci suka yiwa Illa a jihar Zamfara.

 

 

Gwamna ya samu tabbacin ga Mataimakiyar Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya akan ganin an bayar da tallafi na kayan aiki na gaggawa don samun nasara akan yaki da cutar cizon sauro ga mata masu juna biyu da yara kananan da cutar take yiwa saurin lahani.

 

 

 

Sauran sune samar da ingantattun bayanai daga ofishin Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya da zasu yi amfani ga bunkasa hanyoyin kasuwanci da saka jari don ciyar da tattalin arziki jahar zama a gaba.

 

 

Mataimakiyar Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya Amina Mohammed ta baiwa Gwamna tabbaci na zata yi duk abin da ya dace don ganin an taimakawa al’ummar jahar Zamfara, mussaman mata masu juna biyu da kananan yara saboda inganta rayuwarsu da samar musu da rayuwa mai amfani da ci gaba.

 

 

 

Ta jinjina ma Gwamnan Bello Muhammad Mutawalle dangane da kokarinsa na yaki da ayyukan ta’addanci tare da samar da bayanai na gaskiya dake amfani ga yaki da ta’addanci tare da daukar matakai akan fitar da jahar daga yanayin da jahar Zamfara take ciki, abin da ya bude hanyar samar da taimako da agaji da zai taimaki miliyoyin al’ummar jahar Zamfara.

 

 

 

Tun da farko sai da gwamnan jahar Zamfara, Hon Bello Muhammad Mutawalle ya yiwa Mataimakiyar Sakataren Janar bayani dangane da irin yanayin da al’umma jahar suka samu kansu da na yankin arewa maso yamma, dake fuskantar kalubalen rashin tsaro, talauci da ayyukan ta’addanci.

 

 

Ya baiyana cewar, ya samu kwarin guiwa daga goyon baya da ya samu daga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da kuma addu’a da fatan alheri na al’ummar jahar Zamfara akan ganin ya dauki matakai don nemo mafita ga wadanan matsalolin.

 

 

 

Ya nuna godiyarsa ga irin karincin wanda Mataimakiyar Sakataren Janar tayi musu dangane da kyautatawa da kuma samun wannan damar da ta bashi tare da kwarin guiwa akan zuwansa Amurka don ganin an nemo mafita da bayar da gudumuwa mai amfani da zata ciyar da al’ummar Zamfara shekaru masu yawa anan gaba.

 

 

About andiya

Check Also

Ramadan 2023: Nigerian Church Reaches Out To Over 1000 Underprivileged Muslims/ Almajiri.

  The church of Christ Evangelical and life Intercessory Ministry, Sabon Tasha Kaduna State has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.