Home / Labarai / Gwamnatin Masari Ba Ta Hana Yin Amfani Da Dandalin Sada Zumunta Ba

Gwamnatin Masari Ba Ta Hana Yin Amfani Da Dandalin Sada Zumunta Ba

Gwamnati Massri Ba Ta Hana Yin Amfani Da Dandalin Sada Zumunta Ba
Mustapha Imrana Andullahi
Gwamnatin Jihar Katsina Ba Ta Hana Yin Amfani Da Dandali Sada Zumunta Ga Ma’aikata Ba
Wata takardar da ake ta yadawa a dandalin Sada zumunta na yanar Gizo ya jawo hankalin Gwamnatin Jihar katsina kan cewa wai ta hana yin amfani da WhatsApp da kuma Fezbuk domin fadin albarkacin baki ga duk wani ma’aikacin makarantun sakandare.
Kamar dai yadda wata sanarwa daga ma’aikatar ilimin Jihar Katsina ta sanar cewa wannan lamari dai ya shafi wata shiyya ne kawai na ma’aikatar ilimin kuma an yi wannan hanin ne domin magance wadansu matsalolin tafiyar da mulki kawai.
Bisa hakan ne ma’aikatar ilimi ta Jiha ta fitar da sanarwa domin yin cikakken bayani game da takardar da take yawo a yanar Gizo.
A nata bangaren Gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari babu wani lokaci ko kadan ta hana ko kuma takaita yin amfani da kafar Sada zumunta ta yanar Gizo Gizo wani mutum daya ko kuma gungun wadansu mutane saboda yin hakan zai iya haifar da nakasu ga yancin da jama’a suke da shi na yancin da damar amfani da wannan kafa. Saboda haka Gwamnatin Aminu Bello Masari ba ta tauyewa kowa hakkins.

About andiya

Check Also

PRESIDENT TINUBU COMMENDS DANGOTE GROUP OVER NEW GANTRY PRICE OF DIESEL

  President Bola Tinubu commends the enterprising feat of Dangote Oil and Gas Limited in …

Leave a Reply

Your email address will not be published.