Home / Labarai / GWAMNATIN ADAMAWA TA SANAR DA DOKAR HANA FITA SA’O’I 24

GWAMNATIN ADAMAWA TA SANAR DA DOKAR HANA FITA SA’O’I 24

Daga Imrana Abdullahi

 Gwamnan jihar Adamawa  Honarabul Ahmadu Umaru Fintiri ya kafa dokar hana fita ta sa’o’i 24 a jihar, daga nan zuwa ranar Lahadi 30 ga Yuli, 2023.

Wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na gwamnan, Humwashi Wonosikou, ya fitar a ranar Lahadi, ta ce dokar hana fita ta biyo bayan mummunan yanayin da yan Watson kaya suka dauka a babban birnin jihar yayin da suke far wa mutane tare da kutsawa harabar kasuwanci da gidaje suna kwashe dukiyoyi.

Da dokar ta-baci, ba za a yi zirga-zirga a fadin jihar ba.

Honarabul   Fintiri ya ce wadanda ke kan muhimman ayyuka tare da ingantacciyar shaida ne kawai za a ba su damar zagayawa yayin lokacin dokar hana fitar.

Gwamnan ya kuma yi kira ga ‘yan kasa da mazauna jihar da su bi wannan umarni, inda ya kara da cewa duk wanda aka samu ya saba wa dokar za a kama shi kuma ya fuskanci fushin hukumar kamar yadda doka tatanadar.

About andiya

Check Also

NA 8 Div Sokoto new GOC,  General Ibikunle assumes

S. Adamu, Sokoto A new GOC for the 8 Division Nigerian Army, Sokoto , appointed …

Leave a Reply

Your email address will not be published.