Related Articles
Gwamnatin Buhari Na Taimakawa Matasa – Dikko Radda
Alhaji Dokta Dikko Umar Radda shugaban hukumar da ke kokarin kara inganta kanana da matsakaitan masana’antu na tarayyar Nijeriya ya bayyana dalilin da yasa hukumarsa suka shirya gagarumin bikin baje kolin kanana da matsakaitan masana’antu domin Sada su da kamfanoni, Bankin Manoma da sauran manyan cibiyoyin kasuwanci, ya dai bayyana hakan ne a tattaunawarsu da Mustapha Imrana Abdullahi Ayi karatu lafiya.
Garkuwa : Ko zaka bayyana mini dalilin da yasa hukumarka ta shirya wannan taron Baje Kolin masana’antu?
Dikko Radda : Bismillahi rahmanirraheem, wato babban makasudin yin wannan taron baje kolin shi ne domin ta haka ne zamu iya sadar da zumunci tsakanin kanana da matsakaitan masana’antu, kuma wannan abu mun farashi kusan shekara uku da ta wuce kuma kowace shekara muna zabar Jihohi guda biyu daya daga Kudu daya daga Arewa mu kira yan kasuwar wannan wuri su yi shawarwari su kuma yi hulda da mu da sauran hukumomin Gwamnatin da ke bukatar su yi magana da su domin samun mafita a bisa bukatunsu da suke gudanarwa, sannan kuma su samu hanyoyin da za su sayar da kayayyakinsu.
Banda wannan kuma tsarin kuma da muke ce masa samun dama ta hanyar bake koli a cikin gida, akwai tsarin da muke na daukar wasu daga cikinsu mu kaisu kasashen duniya a Kasuwannin duniya na duniya domin su hadu da mutane can su sayar da kayayyakinsu da suka je da su daga Nijeriya suma su sayo wasu kayayyakin da za su habbaka yadda suke gudanar da kasuwancinsu a kasashenmu.
Garkuwa : Wannan karon an samu matsala wajen cutar Korona da ta damu abubuwa da dama, a matsayinku na hukuma da ke bunkasa kanana da matsakaitan masana’antu wane kokari kuke yi mutane su Farfado daga cikin halin da suka shiga?
Dikko Inde : Wato kuma sane da cewa ita Gwamnatin tarayya ta fito da tsarin da ta ware naira biliyan 75 na taimakawa kanana da matsakaitan masana’antu wanda maganar nan da muke yi wasu daga ciki sun fara samun kayayyakinsu su fara samun alamar Banki ko yanzu cikin bayanina na ce ina fatar mutanen Kaduna sun fara samun alat na Banki za kuma mu yi watanni uku muna yi bangare hudu ne akwai wanda ake Tallafawa masu biyan albashin ma’aikatansu akwai masu sana’ar hannu ko Kafinta, Lebura ko wanda ake ba su naira dubu Talatin Talatin akwai wadanda ke tuka motoci, Keke Nafef, Yan Achaba akwai tallafin da za a ba su na naira dubu Talatin wanda satin da ya gabata muka kaddamar da shi.
Sannan akwai batun inganta kamfani ko sana’a da ake ba su fom din hukumar yi wa kamfanoni rajista CAC ayi masu rajistar kasuwancinsu kyauta wannan na cikin tsarin da Gwamnatin tarayya ta fito da shi na ganin cewa an Tallafawa kanana da matsakaitan masana’antu domin su fita cikin wannan kangin na Cutar Korona.
Garkuwa : A matsayinka na shugaban hukumar SMEDAN akwai wadanda za su isar da irin wannan sakon ga jama’a ta kasa?
Dikko Radda : Mun yi amfani da hanyoyi daban daban kamar rediyoyin Jihohi da na tarayya duk mun yi bayanai domin jama’a su ji su kuma amfana. Kuma mun yi amfani da harsuna na gida irinsu Hausa, Yarbanci da Igbo, Fulfulde da kuma turancin buroka duk domin abin nan ya kai kasa.
Kuma a kowace Jiha mun je mun yi taro da shugabannin kungiyoyinsu mun wayar masu da kai mun umarcesu kan cewa su je su wayar da kan Mutanensu yayan kungiyoyinsu da ke kauyuka.
Garkuwa : Nijeriya ta shiga wani yanayin tattalin arziki da lamarin ya ta’allaka ga kananan masana’antu da wasu suke yankunan karkara wane kokari kuke yi domin wadannan kananan masana’antu da ke kauyuka da garuruwa sun samu shiga cikin tsarin?
Dikko Radda : Kusan wannan shi ne babban makasudin da yasa muka fito da wani tsari na rajistar masu kanana da matsakaitan masana’antu, mun fara yin wannan tsarin muna bi kauye kauye, kananan hukumomi muna yin rajistarsu domin in baka yi hakan ba ka tsantsanesu ka tabbatar da cewa sun hau bisa turba da ta kamata to ba zaka iya tantance abin da ke faruwa ba a nan ko a kasar.
Yanzu daga bara da muka fara rajistar nan yanzu haka mun kusa rajistar miliyan biyu, to, in ka lura bangare ne mai yawa akwai wajen mutum miliyan Arba’in da daya da suke gudanar da irin wannan a kasar nan. Kuma wannan kanana da matsakaitan masana’antu suke bayar da fiye da kashi 60 cikin dari na ayyukan da ake yi a Nijeriya kuma a tattalin arziki suke bayar da kashi 48 da digo tara na kididdigar tattalin arzikin kasar nan don haka ba bangare bane da za a yi wasa da ita duk abin da aka ce wajen mutum miliyan Arba’in da daya (41) na yinsa a kasa hakika ba abu ne da za a yi wasa da shi ba domin in ba wannan abin kasar karyewa za ta yi.
Garkuwa : Matsalar tsaro na daya daga cikin abin da ke ciwa Nijeriya Tuwo a kwarya musamman wannan yankin da ka fito na Arewa maso Yamma wane kokari kuke domin ana ganin matasa su suke shiga irin wadannan aikata manyan laifuffuka?
Dikko Radda :Gaskiya ne wannan shi daya daga cikin dalilan da mai girma shugaban kasa ke bayarwa na amincewarsa duk lokacin da aka je masa da wani tsari da zai inganta rayuwar matasa saboda a dauke hankalinsu daga shiga wadansu matsaloli na rayuwa domin babu abin da ke kawo tashin hankali da ta’addanci irin zaman banza domin duk mai zaman banza tunaninsa irin na shedan ne, don haka a koda yaushe domin a Kauda zuciyar mutane daga wannan tunanin yakamata ace matasa ya dace a shigar da su kuma idan ka duba ban da ma hukumar SMEDAN akwai hukumomi da yawa da an fito da tallafi kala kala domin a tallafa wa matasan kasar nan.
Wadannan abubuwan su zamu yi ta yi da jan hankali da kira har muga cewa Allah ya biya mana bukatunmu mutanenmu su samu irin ayyukan da ya dace su rika yi a kasar mu.
Garkuwa : Wane kira kake da shi na ganin cewa matasa sun tashi tsaye ba a mikawa mutum Tallafi ba ya shiga gari ya kashe kudin?
Dikko Radda : Tsakani da Allah yana daya daga cikin abubuwan da ke kawo matsala a kasar nan ana bayar da kudi ayi kasuwanci da abubuwa da yawa na sana’o’i amma mutane na dauke abin da aka ba su na kasuwancin suna yin wasu abubuwa daban. Yanzu akwai abubuwa da dama da zaka ga kun zo kun horar da jama’a da dama kun dauki kayan sana’a kun ba su wasu na waje suna jira idan an zo da kayan sana’ar su saya to, wannan abu dole sai mun dage mun yi abin da ya dace domin kasar mu ta ci gaba har mu ma mu Tallafawa yan uwanmu.
Garkuwa : Akwai tsarin da kuke ba masu Keke Napep, Direbobin Babura, Motoci tallafin Cutar Korona da ka kaddamar a Katsina a wannan Jiha ta Kaduna yaushe ne za a fara yin wannan tsarin?
Dikko Radda : Wato ranar da muka kaddamar da shi a Katsina a ranar ne muka kaddamar dukkan Jihohin Nijeriya guda 36 kuma shiri ne aka yi domin an ga cewa masu wannan sana’ar ba su iya fita suka gudanar da sana’arsu ba lokacin da aka yi kulle, don haka Gwamnati ta ba su Tallafi domin su rage matsalolin da suka shiga ciki naira dubu Talatin in ka dauke ta kaba mai Achaba ko mai tura Kura wani abu ne da zai taimaka masa wajen tafiyar da iyalansa da tafiyar da harkar sana’arsa da kasuwancinsa baki daya.
Garkuwa : To ina za su je su cika wannan Takardar neman tallafin?
Dikko Radda : Wato mun tattauna da yan kungiyoyinsu mun kuma gaya masu cewa duk wanda zai samu wannan abin sai ya kasance yana da tsari guda uku, ya zama dan Nijeriya, ya zamana yana da asusun ajiya na Banki ya kuma kasance shi dan wannan kungiyar ne ko ta yan Achaba, ko ta yan Keke Napep ko ta masu tura Kura ko dai cikin kungiyoyin nasu, sannan kuma ya kasance cewa shi dan Nijeriya ne wannan shi ne ka’idar da ake bukata kuma wanda ma mamba ne na kungiyar ko bai bayar da sunansa ga kungiyar ba to wadanda za su rubuta sunansu ga kungiyar sai ya gaya masu shi dan kungiya ne sai masu rubutawa su rubuta sunansa, kowace Jiha za ta amfana da mutum dubu 4,500 ban da Jihar Kano, Legas da Abiya su sun dara saboda sun fi yawan mutane masu irin wadannan hidimar.
Garkuwa : Me zaka ce game da zargin da wasu ke cewa irin wannan tsarin Tuwona mai na yan siyasa ke yi, sai abokai da yan uwa?
Dikko Radda : Wato abin da yasa wannan tsarin ya bambance saboda tsari ne wanda ake zuwa yanar Gizo ana cikawa in an cike shikenan, na kuma gayawa mutane cewa da shugaban kasa, Gwamna, Minista da ni shugaban SMEDAN ba wanda ke iya taimakawa wani ya samu wanda ya fara zuwa shi zai samu in wuri ya cika ka makara kuma kai ka makara da kanka ba wani ya hana ka ba.
Garkuwa : Mun Gode
Dikko Radda: Nima na Gode kwarai.