…Nan da Sati biyu za a fara aikin garin Tudun biri
Daga Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya bayyana cewa kokarin da yake yi na hadin kan jama’a da ake tafiya tare da kowa ba tare da nuna wani bambanci ba na haifarwa da Gwamnatin Jihar Kaduna nasarori da yawa.
Gwamna Uba Sani ya bayyana hakan ne a cikin wata tattaunawa ta kai tsaye da gidan Talbijin na TVC a cikin shirin tattaunawar da manema labarai ke yi mai suna ( Journalists Hangout)
Gwamna Uba Sani ya ce hakika kasancewarsa na mutumin da ya san shugaban kasa tun can tsawon shekaru sama da Talatin ya san Bola Ahmed Tinubu ya sadaukar domin Najeriya ta samu ci gaba, don haka muna da tabbacin lallai za a samu nasara a kasa kuma shi kansa shugaban kasa zai samu nasarar tafiyar da kasar nan.
“Ni ina tare da kowa ba tare da wani bambanci ba duk kungiyoyin da suka hada da na kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) da jama’atunnasarul Islam (JNI) da sauran kungiyoyi duk ana tare da su da Gwamnatin Jihar Kaduna domin a samu ci gaban da ya dace a Jihar da kasa baki daya.
Gwamnan ya ce mun fitar da gagarumin shirin taimakawa jama’a domin rage radadin batun cire tallafin mai kuma tallafin nan na biliyoyim kudi ne duk za a rabawa jama’a a cikin Jihar kaduna.
“Muna jinjinawa shugaba Bola Ahmed Tinubu a kan batun da ya ce ya na goyon bayan a kirkiri Yan Sandan Jihohi da nufin samun magance matsalolin tsaro”.
” Babu wata matsala a wajen abubuwan da ake bukata wajen samun a dauki mutane Yan Sandan Jihohi domin duk abin da ake nema duk daya ne da na idan ana son a dauki Yan Sanda na Gwamnatin tarayya, don haka ba wata matsala”.
Abin da na fahimta da batun harkar tsaro shi ne aiki ne na kowa da kowa domin a samu ci gaba a koda yaushe, saboda haka ne muka kirkiri gidauniyar kula da harkokin tsaro ta yadda kowa zai samu damar bayar da tasa gudunmawa. Ya dace Gwamnati a kowane mataki ta rika rungumar jama’a baki daya wanda hakan zai taimaka kwarai.
“Mun dauki kyawawan matakan kula da harkokin tsaro na mayar da tarin tattaunawa a kan harkokin tsaro zuwa duk sati biyu, kuma na ta fi wurin manya manyan shugabannin tsaro a Kaduna duk mun tattauna da su. Kuma a nan da wani dan lokaci za mu ba jami’an tsaro karin motoci kuma mun fadada mahalarta tattauna harkokin tsaro a Jihar Kaduna duk da nufin samun nasara”.
Samun hadin kan jama’a sakamakon tafiya da kowa da kowa ya haifar mana da samun wadansu manyan mutanen da ba yan jam’iyyar APC ba duk sun dawo cikin wannan Gwamnatin da nake yi wa jagoranci ana tafiya kuma ana tattaunawa da su.
Kuma a matakin kananan hukumomi ma ana yin taron tattauna harkokin tsaro a duk kowane wata domin a samu hanyoyin mafita da nasarar da kowa ke bukata.
“Muna yin aiki tare da Gwamnonin Jihohin Neja da Katsina domin a samu magance matsalar tsaro ta yadda tattalin arziki zai kara bunkasa.
“Mun yi kasafin kudi a Jihar Kaduna da muka yi wa taken bunkasa yankunan karkara da kuma yin aiki tare da kowa, hakan ya sa muka gina manya manyan wuraren Koyar da sana’o’i a Jihar Kaduna, saboda mun samu nasarar gano cewa akwai matsalar samun
Samarun Kataf, karamar hukumar Soba
Muna yin sababbin tituna 60 da idan mun hada su wuri daya za a ga muna yin aikin tituna masu kilomita a kalla sama da dari biyar ,kuma babban Bankin Afirka na yin aikin yin kyakkyawan gyare gyaren dakunan kiwon lafiya da ake kira ( Primaty health centers) duk kuma Bankin na yin hakan ne kyauta da nufin samun amfanin jama’a.
“Ni ba Gwamnan Musulmi,Kirista ko wani bangare ko kabila ba ne domin na Rantsar zai yi wa kowa adalci don haka ne ma muke da wani kwamitin kungiyoyin JNI da kungiyar Kiristoci ta CAN da suke yin aikin fadakar da jama’a tare, ban samu da ko APC, PDP, jam’iyyar Labo ko dai wata jam’iyya ba kawai abin duba wa shi ne ci gaban kowa da kowa.
Gwamna Uba Sani ya ce nan da sati biyu za a fara aikin ginin garin Tudun Biri kamar yadda shugaban kasa ya yi alkawari