Home / Labarai / Gwamnatin Jigawa Ta Shirya Taron Horas Da Majalisar Zartaswa Da Mukaddasan Gwamnati

Gwamnatin Jigawa Ta Shirya Taron Horas Da Majalisar Zartaswa Da Mukaddasan Gwamnati

Kamar dai yadda zaku iya gani a cikin hotunan nan irin yadda taron horaswar ya gudana a garin kaduna.
Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar tare da Mataimakin Gwamnan Jihar Alhaji Umar Namadi suna halarta taro bita na kwanaki biyu wanda aka shiryawa mambobin majalisar zartaswa tare da wasu daga cikin mukaddasan gwamnati, wanda ake yi a Hotel Seventeen,  na hanyar tafawa balewa, dake jihar Kaduna.
Auwal Danladi Sankara mai taimakawa Gwamnan Jigawa a kan harkokin kafafen yada labarai na zamani da dandalin Sada zumuntar zamani ne ya ruwaito daga dakin taron.
Bitar wanda aka shirya za’a gudanar da ita a ranar 27 da ranar 28 ga watan fabarairu na da taken “tabbatar da dorewar Gwamnati mai inganci ta fuskar bunkasa tattalin da cigaban al’umma”.
Daga cikin mambobin majalisar zartaswa da suke halartar taron akwai Sakataren Gwamnatin Jihar Alhaji Abdulkadir Fanini, da dukkanin Kwamishinoni ma’aikatu, da masu bawa Gwamna shawara da kuma wasu daga cikin mataimaka na musamman ga Maigirma Gwamna.

About andiya

Check Also

Kaduna Church Leaders Visit Imams at Eid Praying Ground to Promote Peace, Love, and Religious Tolerance

    In a remarkable demonstration of interfaith harmony, Pastor (Dr.) Yohanna Buru, a Christian …

Leave a Reply

Your email address will not be published.