Home / Ilimi / Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Cimma Matsaya a Game Da Daliban GGSS Kawo

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Cimma Matsaya a Game Da Daliban GGSS Kawo

Daga  Imrana Kaduna
Babbar Sakatariya a ma’aikatar ilimin Jihar Kaduna Uwargida S Yayi, ta bayyana wa iyayen daliban makarantar Sakandire ta Kawo irin matsayin Gwamnati game da daliban makarantar Yam mata da ke Kawo.
Sakatariyar ta shaidawa taron da suka yi da iyayen yara cewa tuni aka sama wa daliban makarantar Kawo wata makarantar da za su ci gaba da gudanar da karatunsu a makarantar Kwalejin Rimi a cikin garin Kaduna.
“Mun san mutanen wannan wurin masu son jama’a ne kuma wuri ne mai zaman lafiya don haka muka zabi wannan makaranta da kuma makarantar Firamare ta Unguwar Kudu duk a nan Unguwar Rimi”
Sai dai ta yi kira ga iyaye da su ci gaba da kulawa da tarbiyyar yayansu musamman saboda irin labarin da ta ce ta samu na wai ba a shiri tsakanin yaran Unguwar Kudu da yaran Unguwar Kabala duk a cikin Kaduna.
“Hakika iyayen yara na bukatar sai sun tashi tsaye wajen kara inganta tarbiyyar yayansu, ta yaya za a ce wasu basa jituwa da kuma tsawon lokaci a cikin gari daya”.
Ta kara da cewa Gwamnatin Jihar ta yi wannan tsarin ne da kyakkyawar manufa domin dukkan dalibai su samu nasarar yin karatunsu.
Da yake tofa albarkacin bakinsa shugaban kungiyar iyayen yara dalibai Alhaji Haruna Danjuma, cewa ya yi suna bukatar kowa ya zauna lafiya da juna, sannan a ci gaba da bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga Gwamnati ta yadda za ta samu sukunin yi wa jama’a aiki kamar yadda ya dace.
“Ya dace mutane musamman iyayen yara su sani cewa yawan surutai barkatai ba zai kawo ci gaban da ake bukata ba musamman game da batun sama wa daliban makarantar Kawo wurin da za su ci gaba da karatunsu”.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.