Home / Labarai / Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Cire Dokar Hana Fita A Baki Dayan Kananan Hukumomi 23

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Cire Dokar Hana Fita A Baki Dayan Kananan Hukumomi 23

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Cire Dokar Hana Fita A Baki Dayan Kananan Hukumomi 23
 Imrana Abdullahi
Gwamnatin Jihar Kaduna ta amince da cire dokar hana fita da saka Sanya daga karfe 6 na safiyar kowace rana zuwa 6 na Yamma a daukacin kananan hukumomi 23 da ke fadin Jihar baki daya.
Kamar yadda wata sanarwa ta bayyana cewa batun cire dokar zai fara aiki ne nan take.
Ya zuwa yanzu an sanar da dukkan shugabannin hukumomin tsaro game da wannan lamarin. Amma dai za a ci gaba da gudanar da aikin fatirin da Sanya idanu irin na harkokin tsaro.
Wannan bayani na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ke dauke da as hannun kwamishinan kula da harkokin tsaro da al’amuran cikin gida Malam Samuel Aruwan.
Sanarwar ta ci gaba da bayanin cewa Gwamnati ba za ta amince da karya doka da oda ba a kowane irin yanayi.
Saboda haka sanarwar ta shawarci jama’a da su ci gaba da gudanar da ayyukansu na neman abinci kamar yadda suka saba ta hanyar halak kuma su kai rahoton dukkan wani lamarin da suke ganin zai zama barazana ga harkar tsaron Dukiya da lafiyar jama’a zuwa ga jami’an tsaro a Jihar Kaduna musamman ga dakin da aka ware domin karbar sakonni a wadannan lambobin.
09034000060
08170189999

About andiya

Check Also

APC RELOCATES TO NEW STATE HEADQUARTERS IN GUSAU, ZAMFARA

The Zamfara State chapter of the All Progressives Congress APC has today relocated to its …

Leave a Reply

Your email address will not be published.